Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad ta bayar da umarnin hana hukumomin tarayya dakile kason kudaden da ake bai wa kananan hukumomi 44 na jihar duk wata.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, hukuncin kotun ya biyo bayan karar da kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) da sauran mazauna jihar suka shigar a gaban kotun a ranar 1 ga Nuwamba, 2024.
- Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum Kan Zargin Cin Mutuncin Limami A Kano
- ’Yan Siyasar Amurka Na Bata Demokuradiyyar Kasarsu
A cikin umarnin mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Nuwamba, Mai shari’a Muhammad ya bai wa masu shigar da kara izinin mika takardun umarnin kotun ga ofishin Akanta Janar na Tarayya da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Hukumar tsimi da tanadi kan tattara haraji na kasa (RMAFC).
Karar wacce aka shigar, ta nuna damuwa kan yiwuwar hanawa ko kuma jinkirin fitar da kudaden da ake bai wa kananan hukumomi a jihar.
An dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga Nuwamba, 2024.