Dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump, na bukatar kuri’u 24 kawai don lashe wa’adi na biyu a matsayin Shugaban Amurka.Â
Ya zuwa yanzu, Trump ya samu kuri’u 246 na Electoral College, yayin da abokiyar hamayyarsa daga jam’iyyar Democrat, Mataimakiyar Shugaban Kasa, Kamala Harris, ke da kuri’u 210.
- Buhari Ya Kai Ziyarar Jaje Jihohin Borno Da Jigawa
- Xi Ya Taya Boko Murnar Zabarsa A Matsayin Shugaban Botswana
Domin lashe zaben, dan takara na bukatar kuri’u 270 daga cikin jimillar kuri’u 538.
Ana sa ran Trump zai lashe jihohin North Carolina da Georgia, wanda ya kara masa karfi a zaben.
Kamfen din Trump ya mayar da hankali ne kan batutuwan kamar shige da fice da hauhawar farashi, yayin da Harris ta fi mayar da hankali kan hakkokin mata da bunkasa tattalin arziki.
Da yake ana sa ran jam’iyyar Republican za ta karbe ikon Majalisar Dattawa, siyasar Amurka na iya samun sauyi mai muhimmanci.
Duniya na sa ido yayin da wannan zabe mai cike da tarihi ke dab da zuwa karshe.