ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babban Hafsan Sojin Ƙasan Nijeriya, Lagbaja, Ya Rasu

by Sadiq
2 years ago
Sojin

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da rasuwar, Babban Hafsan Sojin Kasan Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ya rasu yana da shekara 56.

Sanarwar da ta fito ne daga fadar shugaban kasa, wadda Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa Lagbaja ya rasu a daren ranar Talata a Legas bayan fama da rashin lafiya.

  • Xi Ya Bukaci A Kara Zage Damtse Wajen Farfado Da Kauyuka
  • Buhari Ya Kai Ziyarar Jaje Jihohin Borno Da Jigawa

An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968.

ADVERTISEMENT

Shugaba Tinubu ya nada shi matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa a ranar 19 ga Yunin 2023.

Ya fara aikin soja a makarantar horas da sojoji ta kasa (NDA), a shekarar 1987, kuma an nada a matsayin Laftanar na biyu a rundunar Infantry ta Nijeriya a ranar 19 ga Satumban 1992, a matsayin wani daga cikin wadanda suka kammala Kwas na 39.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A tsawon aikinsa, Laftanar-Janar Lagbaja ya nuna kwarewa wajen shugabanci.

Ya yi aiki a matsayin mai kula da rukunin sojoji a bataliya ta 93 da kuma 72 ta Special Forces Battalion.

Ya taka muhimmiyar rawa a wasu ayyukan tsaro a cikin gida, kamar Operation ZAKI a jihar Benuwe, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu Maso Gabashin Nijeriya, da kuma Operation Forest Sanity a jihohin Kaduna da Neja.

Lagbaja ya yi karatu a makarantar U.S. Army War College kuma ya samu digirin digirgir a fannin Nazarin Tsare-tsare, wanda ya nuna himmarsa wajen kwarewa da shugabanci.

Ya rasu ya bar mata, Mariya, da ‘ya’ya biyu.

“Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalansa da rundunar sojin Nijeriya.

“Ya yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama,” in ji Onanuga.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
PDP A Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Sadiq Wali Da Abacha

Kotu Ta Hana CBN Da Sauransu Yi Wa Kudaden Kananan Hukumomi Katsa-Landan

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.