Wani binciken kwakwaf kan kuskuren harin sojin saman Nijeriya a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Rann a jihar Borno a shekarar 2017 ya gano da hannun kasar Amurka wajen bai wa dakarun sojin na Nijeriya bayanan sirri da ya kai ga kaddamar da harin na kuskure kan wadanda ba su ji na su gani ba.
Idan za ku iya tunawa dai a kalla fararen hula 160 ne mafiya yawansu kananan yara ne suka mutu a kuskuren farmakin na watan Janairun 2017 wanda Sojin suka yi tsammanin dandazon mayakan Boko Haram ne a wajen.
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok A Borno
- Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Borno
Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda wata jaridar Amurka to intanet ta wallafa wani rubutu a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata, wanda ke bayyana yadda Amurkan ta bayar da bayani ga Sojin Nijeriya game da dandazon ‘yan ta’addan a Rann.
Jaridar ta yi ikirarin bankado wani sakamakon binciken Sojin Amurka da ke bayyana yadda sashen leken asirin kasar ya bayar da bayanan sirri ga Sojin Nijeriyar don kaddamar da harin amma kuma ya zama kuskure, wanda ya kai ga kisan fararen hular.
Bayan fitar hujjojin sakamakon binciken da gwamnatin Amurka ta yi umarnin gudanarwa kan kuskuren harin wanda ya tayar da hankalin duniya, jaridar ta ce an gano umarnin kaddamar da harin ne daga wani babban Janar din Sojin Amurka amma kuma aka gaza fitar da jawabin saboda kaucewa aikata ba daidai ba daga kasar da ake gani a matsayin jagorar karfin Soji a Duniya.