Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sa kai (CJTF) sun kashe adadin mayakan ‘yan kungiyar Boko Haram da dama.
LEADERSHIP ta tattaro cewa da sanyin safiyar Talata ne dakarun Sojoji ta Brigade 21 da ke Bama a Jihar Borno, sun kai farmaki sansanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ke kauyen Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar.
Wani soji ya rasa Rayuwar sa a lokacin da ake gwabzawa da ‘yan ta’addan.
Rahoton sirrin da aka samu daga Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tayarda kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, wanda wakilinmu ya samu, yace wannan farmakin ya yi sanadiyyar kawar da ‘yan ta’addan da dama.
Majiyar ta ce, “Mun kashe da yawa daga cikinsu a kan ruwa, wasu daga cikinsu sun yi kokarin yin artabu amma mun fatattake su, yayin da wasu kuma suka tsere.
“An ga gawarwakin ‘yan ta’addan da dama a ko’ina.”
Sai dai majiyar ta kara da cewa, “Soja daya ya rasa ransa a lokacin artabun..”