Shugaban hukumar yaki da karya tattalin arzikin kasa da cin hanci da rashawa a Nijeriya (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yi kiran kara inganta alakar aiki a tsakanin hukumarsa da hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS) wajen yaki da masu aikata lmzagon kasa ga tattalin arzikin kasa da dangogin laifukan rashawa a Nijeriya.
Wannan bayanin na kunshe a cikin wata sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar lura da shige da fice, ACI Amos Okpu ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta nakalto cewa Shugaban hukumar EFCC ya yi wannan kiran ne a lokacin da suke ganawa da Kwanturola Janar nahukumar kula da shige da fice ta kasa Isah Jere a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, Bawa “Ya zo shalkwatar hukumar ne domin neman karin goyon baya da hadin kai wajen yaki da dukkanin nau’ikan laifukan da suka shafi aikata rashawa da zagon kasa ga tattalin arzikin kasa a ciki da wajen kasar nan musamman ta kan iyakokin kasarmu”.
Ya ce, NIS tana sahun gaba a cikin hukumomin da suke yaki da harkallar rashawa don haka ne ya nemi hukumar da ta kara amfani da dabarun aikinta da amfani da na’urar zamani ta ICT wajen taimakon hukumarsa don kara bunkasa yaki da cin hanci da rashawa.
Abdulrasheed ya kuma sake yin kira na neman hadin kan hukumar a bangaren bibiya da kama wadanda ke kokarin ficewa da kudin da suka mallaka ta hanyar cin hanci da rashawa, sai ya nemi karin goyon baya kan hakan.
Da ya ke maida jawabi, Kwanturola Janar na hukumar kula da harkokin shige da fice (NIS), Isah Jere, ya ba da tabbacin hukumar na yin aikin hadin guiwa da dukkanin hukumomin da suka dace wajen kokarin kare tattalin arzikin kasar nan.
Isah ya ce a matsayinsa na shugaban hukumar shige da fice, hukumar ta samar da na’urorin zamani da ke taimaka musu wajen tabbatar da cewa duk wani da ake zargi ko aka hana shi fita bai samu damar fita daga cikin kasar nan ta iyakokin kasar ba har sai an tantance tare da amincewa da fita ko shigarsa.
“Muna da na’urorin da kai tsaye cikin ‘yan dakika za su ba mu bayanan tarihi da motsin mutanen da ke son shiga ko fita a iyakokin kasarmu, don haka cikin sauki za mu hana mutumin da ke da wani tabon da ka iya hana shi fita ko shiga damar yin hakan”.
Ya nemi a dauwamar da aikin hadin guiwa tsakanin NIS da EFCC domin samun nasarar da aka sanya a gaba a kowani lokaci.