Gwamnatin jihar Kano dai ta fito fili ta musanta ikirarin cewa ta karbo bashin Naira biliyan 177 daga hannun masu bayar da bashi a kasar Faransa, inda ta bayyana zargin a matsayin Adawa da kuma Siyasa.
Darakta Janar na ofishin kula da basussuka na jihar Kano, Dakta Hamisu Sadi Ali, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Talata, inda ya bayyana cewa, ba a sake karbar wani sabon rance ba tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf kan karagar mulki a watan Mayun 2023.
- ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 10 A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Jigawa
- IPMAN Da Matatar Dangote Sun Kulla Yarjejeniya Kan Dakon Mai Kai-Tsaye
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wata kafar yada labarai ta ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta samu lamunim kudade daga kasar Faransa.
“Ma’aikatar kula da basussuka ta jihar Kano, ba ta da wata masaniya kan karbo wani sabon lamunin kudi, bashin da ake bin jihar, gaba daya wanda sabuwar gwamnati ce ta gada daga wacce ta gabata,” in ji Dokta Ali. Ya bayyana cewa, bashin da ake magana a kai ya samo asali ne daga yarjejeniyar lamuni da aka yi a shekarar 2018 a lokacin gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Dakta Ali ya kara da cewa, gwamnati mai ci ta mayar da hankali ne wajen biyan basussukan da ake bin jihar. “A shekarar 2024, an biya bashin Naira biliyan 63.5, wanda hakan ya rage bashin jihar Kano zuwa Naira biliyan 127.8 a watan Yunin bana.”