A jiya Litinin ne wata mota ta fada cikin wasu mutane dake bin gefen hanya, ta kuma kade da dama daga cikin su, a kusa da filin wasa na yankin Xiangzhou na birnin Zhuhai dake lardin Guangdong. Rahotanni sun ce kawo yanzu, adadin mutanen da motar ta hallaka sun kai 35, baya ga karin wasu 43 da suka ji munanan raunuka.
Bayan aukuwar hakan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya dora muhimmancin gaske kan lamarin, inda ya ce abun bakin ciki ne ganin yadda wannan lamari ya haifar da rasuwar mutane da dama, cikin wani yanayi mai matukar tayar da hankali. Ya ce, “Wajibi ne mu yi duk mai yiyuwa wajen jinyar wadanda suka ji raunuka, da kwantar da hankalin su da iyalan su. Dole ne mu tsaurara hukunci ga wanda ya aikata wannan ta’asa gwargwadon doka.”
Shugaba Xi ya kara da cewa, ya zama dole dukkanin yankuna da sassa masu ruwa da tsaki, su koyi darasi daga wannan lamari, su karfafa matakan kandagarki da shawo kan hadurra, da warware sabani da rigingimu a kan lokaci, kana a dakile aukuwar abubuwa masu tayar da hankali, tare da yin duk mai yiyuwa wajen kare rayukan al’umma, da wanzar da daidaito a zamantakewar al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)