Ma iya cewa tauraron nahiyar Afirka na haskakawa, a wajen taron kolin kungiyar G20 dake gudana a kasar Brazil, ganin yadda kungiyar kasashen Afirka AU take halartar taron a matsayin mambar kungiyar G20 a karon farko, kana shugaba Bola Tinubu na kasar Najeriya shi ma ya halarci taron bisa gayyatar da aka yi masa. Ban da haka, kasar Brazil mai karbar bakuncin taron tana kokarin daidaita wasu ayyuka tare da kasar Afirka ta Kudu, ganin yadda Afirka ta Kudun za ta zama mai jagorantar kungiyar G20 a karba karba a shekarar 2025 mai zuwa.
Hakika yin amfani da dandali na G20 wajen shiga ayyukan kula da al’amuran kasa da kasa ya dace da muradun kasashen Afirka. Saboda cikin Ajandar shekarar 2063 ta kungiyar AU ma, an riga an bayyana burin kungiyar na shiga a dama da ita a karin harkokin kasa da kasa. Sa’an nan a taron G20 na bana, shugaban karba-karba na kungiyar AU, kana shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ghazouani, ya yi jawabi, inda ya yi kira da a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, a kokarin raya fasahar noma mai dorewa, da bangaren jin dadin jama’a, da na ilimi, da kayayyakin more rayuwa, don neman cimma burin kawar da yunwa da talauci.
- Kotu Ta ÆŠaure ÆŠan TikTok Watanni 32 A Gidan Yari
- Kotu Ta Wanke Kwamishinan Jigawa Daga Zargin Zina
Ban da haka, a wajen taron G20 na wannan karo, an kimtsa sosai domin taron koli na G20 da zai gudana a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2025. Inda a karkashin taken taron na ”karfafa hadin kai, da daidaituwa, gami da neman ci gaba mai dorewa”, za a fi dora muhimmanci kan matsalolin da suka hada da talauci, da rashin guraben aikin yi, da rashin daidaito a cikin al’umma, da dai sauransu.
A zahiri ne, ko a yanzu, ko a nan gaba, kasashen Afirka sun fi bukatar samun ci gaban tattalin arziki, kuma suna neman kare hakkin raya kai na daukacin kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka. Wannan yunkuri ya zama daya da burin kasar Sin.
A wajen taron kungiyar G20 na wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken ”Gina duniya mai adalci da ake iya samun ci gaba na bai daya”, inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su inganta fannonin ciniki, da zuba jari, da hadin gwiwa a kokarin raya kasa, ta yadda karin kasashe masu tasowa za su iya zamanantar da kansu. Ban da haka ya bukaci a nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa don su shiga a dama da su ta fuskar raya fasahohin zamani, da na kare muhalli, don neman rage gibin da ake samu tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa. Haka zalika, a cikin matakai guda 8 na tallafawa kokarin raya duniya, da kasar Sin ta dauka, wadanda shugaba Xi na kasar Sin ya ambata a ciki jawabinsa, akwai ”Taimaki kasashen Afirka a kokarinsu na raya kansu” da ”Yafe wa kasashe marasa karfin tattalin arziki da suka kulla hulda da Sin harajin kwastam kan dukkan kayayyakin da suke neman sayarwa a kasuwannin Sin”, gami da ”kaddamar da shawarar hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha cikin ‘yanci, don baiwa kasashe masu tasowa damar more sabbin fasahohin da aka kirkira a duniya”, da dai makamantansu.
Duk a wajen taron wannan karo, shugaba Xi na kasar Sin ya yi wani jawabi kan batun yin gyare-gyare kan tsarin kula da harkokin kasa da kasa, inda ya ce ya kamata a kara yafe wa kasashe masu tasowa bashin da ake bin su, ko kuma tsawaita wa’adin biyan bashin. Ya kuma jaddada bukatar kara wakilcin kasashe masu tasowa a fannin kula da ayyukan hada-hadar kudi, da bukatar kasashe masu sukuni da su magance gyara manufofinsu na kudi yadda suka ga dama, tare da haifar da mummunan tasiri kan tattalin arzikin sauran kasashe.
Watakila za ka so ka yi tambaya cewa, ina dalilin da ya sa kasar Sin ke son ganin ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa? Hakika dalili shi ne tunanin kasar a fannin hulda da sauran kasashe, na gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma. A ganin Sinawa, ci gaban tattalin arizkin sauran kasashe shi ma zai amfani kasar Sin. Saboda haka shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ce kasar Sin na son hadin gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa a kokarin samun zamanantarwa ta bai daya. Ya kuma yi amfani da misalin Sin na fitar da jama’arta miliyan 800 daga kangin talauci wajen karfafa gwiwar kasashe daban daban, inda ya ce, ”Kasar Sin ta cimma nasara a wannan fanni, sauran kasashe masu tasowa su ma za su iya tabbatar da hakan.” (Bello Wang)