Jigo a jam’iyyar APC a Kano, Ilyasu Kwankwaso, ya yi kira ga kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) da ta mayar da hankali wajen magance dimbin matsalolin da Arewa ke fuskanta wadanda suka hada da ‘yan bindiga, garkuwa da mutane maimakon kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.
Kwankwaso ya kuma shawarci kungiyar ACF da ta fara tattaunawa da shugabannin addini da na gargajiya da na siyasa a yankin don nemo mafita ga irin ɗimbin matsalolin da ke addabar yankin.
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudurin Wa’adi Guda Na Tsawon Shekara 6 Ga Ofishin Shugaban Ƙasa
- Shari’un Zabe: A Kauce Wa Tarzoma Duk Yadda Ta Kaya
Jigon na APC ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Kano yayin da yake mayar da martani kan sakamakon taron kungiyar ACF da aka gudanar a Kaduna inda aka fitar da wata sanarwa da ta caccaki gwamnatin tarayya bisa zargin rashin kula da yankin.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, ACF ta fitar da sanarwar ne a karshen taronta na majalisar zartarwa ta kasa da ta gudanar a Kaduna a ranar Laraba, inda ta nuna rashin gamsuwarta da manufofin tattalin arziki na gwamnatin Tinubu, inda ta bayyana cewa sun kara tsananta halin kuncin da talakawan Nijeriya ke ciki.
Sanarwar wacce Sakataren Yada Labarai na ACF na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ta yi tsokaci ne kan irin raunin da yankin Arewa ke fama da shi, inda ya yi nuni da cewa, al’ummar yankin na fama da yunwa, karancin ilimi da horar da sana’o’i, da kuma dogaro ga kananun sana’o’i don neman tsira.