Wani yaro Samuel Onyeme mai shekaru 17 ya sha dukan tsiya tare da kulle shi a cikin kejin kare saboda ya ziyarci wata abokiyar karatunsu, Miss Anastasia Celestine.
PUNCH Metro ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Onyeme ya ziyarci abokiyar karatunsa a gidanta da misalin karfe 6 na yamma.
- Mai Keta Hakkin Bil Adam Na Ikirarin Kare Shi
- Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekara-shekara Don Bayyana Kokarinta Na Kare Hakkin Dan Adam
Mahaifiyar yaro, Misis Onyeme, ta shaida wa wakilinmu cewa ya fi kyau ta samu kyakkyawar tarba a gidan Mista Celestine.
Ta ce, “Dana Samuel, dan shekara 17 a duniya yana karatu a Babbar Sakandaren Redeemers International High School, Asaba, Jihar Delta, ya ziyarci abokiyar karatunsa, Anastasia Celestine, a gidanta bayan ta gayyace shi.
“Dana ya ce suna tattaunawa a wajen gidan Mista Celestine lokacin da mahaifinta da ’ya’yansa maza biyu suka hau shi da duka yi masa mugun rauni, ya ce sun yi amfani da katako sannan suka kulle shi a cikin kejin kare.
“Sun kwace wayarsa suka kira ni (mahaifiya), da isowata, na yi kokarin ganinsa amma suka hana ni ganinsa na tsawon awanni biyu.”
Ta ce ‘yarta Jessica, wacce ke waje tana kokarin neman taimako, ita ma ‘yan gidan Celestine sun fuskanci hari a lokacin da ta yi kokarin sake shiga harabar gidan.
“Al’amarin ya ta’azzara sa’ad da Ben, dayan ’ya’yana, wanda shi ne dan’uwa ga Samuel, ya tuntubi wani abokinsa, wanda kuma ya yi magana da wata kungiyar kare hakkin bil’adama kafin su kai ga ’yan sanda, sai aka tara jami’ansu don ceto Samuel daga kejin kare, misalin karfe 10:00 na dare.”
Da yake karin haske, wani mai rajin kare hakkin bil’adama, Mista Bictor Ojei, wanda ya kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar ‘yan sandan Jihar Delta a ranar Talata, ya ce ya tattara ‘yan sanda kafin a kubutar da Samuel daga kejin kare, ya kuma bayyana lamarin a matsayin dabbanci da rashin tausayi.
Ojei, a cikin wata takardar koke ga kwamishinan ‘yan sandan Jihar Delta, ya bukaci da a gaggauta gudanar da bincike tare da gurfanar da Mista Celestine da ‘ya’yansa maza bisa laifin yin garkuwa da su, tsarewa ba bisa ka’ida ba, cin zarafi, da yunkurin kisan kai bisa tanadin dokar laifuffuka ta Nijeriya.
Koken dai ya mika kwafi ga babban Lauyan Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Delta a Asaba da kuma Kodinetan Hukumar Kare Hakkokin Dan’Adam ta kasa reshen Asaba Jihar Delta, inda ta bukaci a yi adalci.
“Wani Onyeme Ben ya tuntubi wani abokinsa, wanda shi ma ya tuntubi kungiyarmu. Bayan rahoton da muka samu ga rundunar ‘yan sandan Jihar Delta, ta tattara jami’ai, kuma an ceto Master Onyeme Samuel daga kejin kare da misalin karfe 10:00 na dare.
“Bisa bayanan da ke sama, Mista Celestine da ‘ya’yansa sun aikata laifukan da suka hada da tsare Misis Onyeme Onome ba bisa ka’ida ba har na tsawon sa’o’i biyu ba tare da iznin ta ba, da kuma tsare Master Onyeme Samuel a cikin kejin kare daga karfe 6:00 na yamma zuwa 10 na dare wanda ya saba wa sashe na 364 na dokar laifuka.
An ruwaito cewa wanda lamarin ya shafa, Samuel, a yanzu haka yana karbar magani a Asibitin kwararru na Asaba, sakamakon raunukan da ya samu yayin da lamarin ya faru.