Babban Daraktan Hukumar Kula da Fitar da kayayyakin masarufi ta Nijeriya, NEPZA, Dakta Olufemi Ogunyemi, ya ce aikin masakar Lekki a yankin Eyin-Osa da ke Epe a Jihar Legas, zai samar da ayyukan yi kai tsaye 5,000 da wasu kuma kimanin 20,000 idan an kammala masakar.
Ogunyemi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake raba kudin tukuici ga iyalan Eyin-Osa guda bakwai da suka bayar da kadada 240.09 ga gwamnatin tarayya domin aikin.
- An Sake Tallafa Wa Al’ummar Gambaru Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
- Takaddamar Rarara Da Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano: A Ina Gizo Ke Sakar?
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da shugaban NEPZA ya yi sannan shugaban sashin mu’amala da jama’a, Martins Odeh ya fitar, a ranar Lahadi a Abuja.
Ogunyemi, wanda ya samu wakilcin Misis Chika Ibekwe, Daraktar ayyuka ta shiyyar, ta ce, al’ummar yankin za su ci gaba da cin gajiyar wannan aiki, inda ta kara da cewa alfanun da za su samu ta hanyar bayar da wannan kadada zai wanzu har kan jikoki da tattaba kunne.