Kasar Sin za ta samar da jiragen sama na lantarki masu tashi da sauka irin na ungulu wato eVTOLs 100,000, a matsayin motocin iyali ko taksi masu tashi a iska nan da shekarar 2030, a cewar wani rahoto da kawancen tattalin arziki masu nasaba da shawagi a kusa da doron kasa ta kasar Sin ya fitar a yau Laraba.
Rahoton ya yi hasashen cewa, ana sa ran za a samar da adadi mai yawa na eVTOLs a kasuwa don rage tsada, da baiwa jama’a damar samun motocin.
- Xi Ya Bukaci A Aiwatar Da Kudurin Kwamitin Sulhun MDD Kan Batun Palastinu
- An Bude Bikin Baje Kolin Samar Da Kayayyaki Na Duniya Na Kasar Sin Karo Na Biyu A Beijing Domin Karfafa Hadin Gwiwa
Kawancen ya yi hasashen cewa, nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa, manyan biranen kasar Sin za su kammala hanyoyin sufuri na sama, da kuma ababen more rayuwa na ba da hidimomi masu nasaba da motocin masu tashi a iska a doron kasa.
Ana sa ran fasahohin da suka hada da kirkirarriyar basira, da ma’amalar dan Adam da kwamfuta, da shimfida hanyoyi masu ba da hidimar intanet, za su saukaka aikace-aikacen wadannan motoci masu tashi a iska marasa matuka, a cewar rahoton. (Mohammed Baba Yahaya)