“Ainihin sunan Tafa ya samo asali ne daga wani kogi, kogin Tafa da ke kusa da garin, wanda a lokacin da iyayenmu, da mu, muka zo wurin, wato inda Tafa take yanzu, babu komai sai kungurumin daji.
Ba gida ko daya, balle bil Adama.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan
- Jami’an Amurka Na Zuzuta Batun Tarkon Bashi Ne Domin Haddasa Rigima
Mu masunta ne, da muka taso daga can garin Bankure ta jihar Kano, a 1965 da nufin yin, Su, wato kamun kifi a wannan rafi mai suna Tafa. Ba gida ko daya. Sai daji kawai, wanda duk cikin dajin babu komai sai namun daji iri-iri ”
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin Malam Shehu Sulaiman, Goran Tafa (Dagaci), a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa a fadarsa da ke garin Tafa, da take cikin karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna a makon jiya.
Akwai abubuwa da dama wadanda mutane ba a sani ba game da wannan gari da ya yi suna a hanyar Abuja zuwa Kaduna saboda ganin da ake masa na shalkwatar holewa da rakashewa.
A tarihin da Goran Tafa ya bayar, ya ce, su biyar suka taso daga Kano don yin sana’ar Su (kamun kifi) a 1965, yana mai cewa ” Shekara daya kafin a kashe su Sardauna muka zo don yin Su”.
Da farko, sun yada zango ne a wani gari mai suna Panda ta cikin Keffi inda suka yi shekara hudu a garin. Daga nan, suka gangaro zuwa Kubaca ta Kagarko, daga nan kuma, a 1965, suka iso wani babban daji kusa da Kogin Tafa a matsayin masunta, “A lokacin mulkin Shagari,” in ji shi.
To idan sun yi Su (kamun kifi), sai su je wata kasuwa mai suna kasuwar Isa a can gaba da rafin Tafa su kwana.
Da tafiya ta yi tafiya, a cewar Goran Tafa Malam Shehu, suka ga ya kamata su samu wurin rayuwa ta din-din-din, inda suka yanke shawara su tuntubi Sarkin Kagarko na wancan lokacin.
To sai shi Sarkin ya aika da su zuwa wajen Sarkin Minna wanda ya ba su izinin su zabi wurin da zai yi musu dadin zama. Sai suka dawo dajin kusa da Rafin Tafa, suka yada zango a wurin, suka fara gina mazauni.
A kwana a tashi, suka share fili sosai bayan sun yi aiki tukuru, suna sassare bishiyoyi da itatuwa. Bayan kwana da kwanaki, suka yi nasarar giggina muhallinsu. Haka aka kafa Garin Tafa.
Ya tuna da cewa, cikin ikon Allah, da kuma rokon shi, suka soma samun baki, masu bukatar wurin yin gini don zama. ”
Ai, mu tunda muna neman wuri ya zama gari, sai muka yayanki filaye, mutane na ta gine-gine, suna zama. Kafin wani dan lokaci, dajin ya kau, alkarya ta ginu. Wannan dajin, shi ne garin Tafa a yau, wanda mu ne muka kafa ta, mu biyar kacal, yau kusan shekaru 50 kenan “.
Da aka tambaye shi ko me ya sa garin Tafa ya yi kaurin suna, musamman game da mata masu zaman kansu, sai Malam Shehu ya yi bayanin cewa, lamarin ya samo asali ne daga garin Gauraka inda a wancan lokacin ya yi mugun kaurin suna a kan alfasha iri-iri kamar sata, karuwanci, shayeshaye, da sauransu. To da abin
ya kai intaha, ya kazanta ainun, sai Gwamnan Jihar Neja (dan jam’iyyar NPN) a wancan lokacin ( 1979-1983), wanda shi ne Sarkin Suleja na yanzu, wato Alhaji Muhammad Auwal Ibrahim, ya ba da umarni a yi rusau, a kuma kori karuwai da su ‘yan daudu da ire-iren su gaba daya, su fice daga garin, su san inda dare ya yi musu.
” To, ina suka dosa mafi kusa da su, kawai sai suka gangaro wannan garin namu Tafa. Duk da shike muna begen baki, gari ya cika, amma gaskiya ba ta irin wannan yanayi da tsari ba; ” in ji shi, yana mai cewa, to yaya suka iya! Dole suka rungumi bakin, suka kuma rungumi kaddara, yana mai cewa, ” babu abin yi, sai muka dukufa rokon Allah, ba dare, ba rana, da muka farga lamarin na son ya rikide zuwa kamar yanayi irin na Gauraka, garin da aka tarwatsa saboda ayyukan assha. Amma alhamdu lillahi al’amarin ya sauya, tunda an samu sauki. Babu tashin hankali a Tafa, matasa ba sa fitina, haka ma karuwai, ko wacce ta kama sana’a don neman na kanta, musamman sayar da abinci da wanki da guga, kuma da yawa sun bar garin, ba kamar da ba. Babu ‘yan daudu, haka shaye-shaye tsakanin matasa sun ragu ainun.
Babu fadace-face tsakanin matasa ko mazauna gari kamar a wasu wurare, ko da shike bincike ya nuna, yanzu akwai gadajen mata nan da can a garin Tafa, amma ba su kai kashi 30 bisa 100 ba, kamar a baya can, inda kusan kashi 60 bisa 100 na gidaje da wuraren assha sun mamaye ko ina. Yau, akwai manyan ma’aikatan Gwamnati a Tafa.
Akwai manyan ‘yan kasuwa, ga kuma manya-manyan malaman addinin Musulunci da manyan Fasto-fasto na addinin kiristanci.
“Saboda haka, mun gode Allah da ya karbi addu’armu. Yau a Tafa, babu yaren da babu, akwai Hausawa da Yarabawa da Fulani da Ibo-ibo da Kanuri da Gwarawa da Katafawa da al’ummah dabandaban da suka fito daga sassan Nijeriya da dama, kuma ana zaman lafiya, babu tsangwama, ana zaune lafiya Musulmi da Kirista, in banda dan abin da ba za a rasa ba, wannan kuma yau da gobe ce sai Allah kamar yadda za a samu a wasu wurare,’’ in ji Dagacin na Tafa.
Ko shakka babu, ana kyakkyawar zamantakewa a Tafa. Sai dai Malam Shehu ya yi kukan cewa, basu da hanyoyi da magudanar ruwa da ruwan sha a garin, kuma gwamnati ba ta sa su cikin tallafin da ta kan yi wa al’umma a Jihar ba.
“Don haka, ina kira ga Gwamnatin mai Girma Gwamna, Malam Nasiru El-Rufa’i, da ya tuna da mu wajen tallafin da gwamnatinsa ke yi duk lokacin da tsarin ya taso. Mu mutanen Tafa, masu bin doka da oda ne, muna da masu sana’oi iri-iri, kuma masu shi suna biyan harajoji tun daga karamar hukuma har zuwa jiha.
A kuma baiwa matasan mu aiki, akwai masu ilmin difloma, da NCE har masu digiri muna da su, ” in ji shi.
Malam Shehu ya ce, ita wannan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna an fara gina ta ne a 1981, aka fara zuba kwalta 1982, yana mai cewa, yau babban titin duk da yana neman gyaran Gwamnatin Tarayya, yana da tasiri musamman ga direbobin Tireloli da tanka-tanka, wadanda suke yada zango a ko yaushe a Tafa, kuma kullum abin karuwa yake yi tunda ta zame musu al’ada, yana mai cewa, “amma kuma, zuwa suna yada zango da jerin motocin nasu, alheri ne a nan Tafa, saboda a nan za su ci abinci, su kwana a loja-loja, kuma duk biya suke yi. To ka ga wannan riba ce gare mu.
Kuma kaga akwai babbar Defo inda wasu da yawa ke faka manyan motocin nasu, kuma duk rana suna biyan kudin shiga, wanda ake amfani da shi “.
Malam Shehu ya kara da cewa, saboda kaurace wa barazanar ‘yan ta’adda ne da suka addabi wurare kamar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna da Jihar Nasarawa da kuma Jihar Neja, ya sa direbobin suka fi amincewa da Tafa, yana mai cewa, “idan da duk wadannan jihohi da wasu wurare cikin Jihar Kaduna za su samu kyakkyawan tsaro daga hare-haren ‘yan bindiga da zaman lafiya kamar Tafa, da duk sauran al’umma, sun rinka tafiyar da harkokinsu na yau da kullum a tsanake, kuma su yi barcin su idanuwansu a rufe”.
Ya tuna tun kafa garin Tafa, ba su tana fuskantar fitina ko tashetashen hankali ba, in ban da wata gobarar tanka da ta jefa mutane cikin rudani da tashin hankali, “Amma a ce fitina ko fadace-fadace a tsakanin al’umma, babu a nan”.
Ya kuma gode wa Gwamnatin Jihar ta Kaduna da ta gina musu asibiti, da makarantun Firamare da na Sakandare a garin, kuma suna ci gaba har yanzu. Amma Goran ya yi takaicin yadda wasu jami’ai za su zo wurin su, su ce wai su daga Abuja, ko daga Gwamnatin Kaduna, ko karamar hukuma suke, su ba su fom su ciccika da nufin za a kawo musu tallafi, amma da zaran sun tafi, basu kara ganin su”.
Haka zalika, ya ce,” ko daukar matasa aikin Soja, ‘Yansanda, ko Sibil Difens, babu wani matashin Tafa da ya taba samu, “Don Allah wannan abu da dadi?. Ai kamata ya yi a tafi tare da mu a cikin ko wani tsari na gwamnati, tunda mu ma ‘yan Nijeriya ne “.
Ya danganta zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa a Tafa ga addu’ar kawar da masifa wanda Musulmi da Kiristoci suke ta yi a kullum, yana mai cewa,
“Ba inda ake addinin Musulunci a duk kananan Hukumomin Jihar Kaduna kamar yadda ake gudanarwa a Tafa. Haka ma addinin Kiristanci, kuma an zama daya, ana ta ibada duk mutane ba su san da wannan ba, su yi ta aibanta Tafa. Su shigo mana su gani “.
Ya ce yau a Tafa, akwai manyan Masallatan Juma’a guda biyar, da Masallatan hamsu salawat sama da 75. Akwai kuma makarantun Tsangaya 80, ga kuma Makarantun Islamiyya ta ko ina ciki da kewayen gari. Sai kuma Coci-coci sama da 20 inda Kiristoci yawancin su ‘yan kudu, suke gudanar da addininsu.
Ya kara da cewa “Kuma duk daren Juma’a, ana sauke Al’kur’ani mai girma don zaman lafiya ta dore, kuma alhamdu lillahi”.
Ya gode wa shugabannin addinan biyu (Musulunci da Kirista) saboda abin da ya kira “Jihadin da suka yi don tabbatar da zaman lafiya a Tafa da ci gaban ta “. Ya yi kuma kira ga jama’ar garin da su ci gaba da irin Kyakkyawar zamantakewa a tsakanin su.
Zagayawa cikin garin Tafa, tana da wuya amma tana da muhimmanci, saboda mutum zai gane yadda yanayin garin yake, da yadda mutane suke rayuwarsu da irin tunanin su. A gaskiya ne, al’ummar garin masu son tsabta ne da neman na kansu, amma sai dai sam, ba su mori ababen more rayuwa ba, musamman hanyoyi, ko ina ka zaga, cabi ne kawai da laka idan an yi ruwa.
“Mu dai a nan, mun dogara ga Allah ne kawai babu kome na jin dadin dan’adam. Ba mu da hanyoyi bamu da magudanar ruwa, kai gasu nan ba iyaka”, wannan kalami ne daga bakin daya daga cikin dattawan Tafa,
Malam Garba Wanzam, shugaban kungiyar ‘yan Acaba, wato Zaman Lafiya Okada Association, Tafa, a lokacin da yake tofa albarkacin bakin shi a kan Tafa.
Mallam Garba ya tuna cewa, a lokacin da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya zo kamfen din shi a Tafa, mutanen da suka tarbe shi, ba iyaka, mata da maza, manya da yara, har matasa suka nuna mishi da tawagar shi bajinta iri-iri, a kan babura da tireloli da keke Napep. Wasu matasan ma, suka kwan-kwanta a kan kwalta, suna kusumbolo, ana musu kida suna ta nuna bajintarsu, duka saboda murnar zuwan ElRufa’i. A lokacin Gwamnan ya yi matukar farin ciki, kuma ya yi mana alkawuran abubuwan jin dadi iri-iri, kafin su koma. Ya kuma ci zabe, amma tun hawansa kujerar Gwamna, mu ba mu taba moriyar wani abin azo a gani daga gwamnatin shi ba.
Makaranta, Asibiti, tun kafin hawan shi ne. To, duk da haka muna kaunar shi dari bisa dari. Amma gaskiya ya zo ya yi mana wani abu kafin ya sauka, ko don irin zaman lafiyar da ta dore a Tafa, da bin doka da oda, ba kamar a wasu wurare ba “.
Garba Wanzam wanda ya ce shekararsa 20 a Tafa. Ya ci gaba da cewa, duk yadda mutane suke wa Tafa mummunan fahimta, to idan sun shiga cikin garin za su yi mamakin yadda yanayin garin da rayuwar al’ummah suke a Tafa. ” Tsarkakakkiyar rayuwa ce, ba kamar yadda wasu suke da jahilcin fahimta ba “, in ji shi.
Haka shi ma Mallam Lawan mai wanki da guga, ya nuna bakin ciki yadda gwamnati ta manta da Tafa, duk da halin dattakon mutanen garin masu bin doka, masu kuma zaman lafiya.
Haka za a yi ta ji idan mutum ya zagaya cikin garin Tafa, wato koke-koke a kan bukatun dan Adam na yau da kullum, kamar yadda Malam dan Bayero da Malam Saminu Tafa da Malama Mairo Iliya da Mr. Nicholas Ndubisi da Mr. Ola John da sauran wasu mazauna garin Tafa suke ta kokawa.
Da yake karin bayani a kan garin Tafa, dan wanda ya fara shugabancin Tafa, Alhaji Yahaya Adamu Nasidi, wanda shi ne Dagacin Tafa ta Yamma a yanzu, ya ce
masarautar ta Tafa ta kasu gida biyu ne.
Shi yana matsayin Dagacin Yammacin Tafa ne, sannan kuma, kawunsa Alhaji Shehu Sulaiman, shi ne Dagacin Gabashin Tafa. Ya ce, lalle iyayen su biyar ne su ka zo Tafa daga can Bunkure ta Kano don yin Su (kamun kifi) kuma suka ga wurin na da ni’ima, ga babban kogi, sai suka yanke shawarin yada zango a kusa da rafin, wanda sunan shi kogin Tafa. Ya ba da sunayen mutum biyar din da suka kafa Tafa kamar haka: Malam Adamu Sulaiman wanda shi ya Fara Hakimi a Tafa, sai Ibrahim Sulaiman, Shehu Sulaiman, Bala Sulaiman, da kuma Abdullahi Sulaiman; “Wadannan su suka kafa Tafa, kuma duk zuriyarmu ne, kuma cikin 1965 shi Adamu Sulaiman ya zo da wadannan ayari”.
Yahaya Adamu Nasidi ya kara da cewa, da farko sun yada zango ne a wani gari mai Suna Dutsen Mata, suka isa Kubaca, daga nan sai suka gangaro dajin da ke kusa da Kogin Tafa, kogin da ya ce ya sha tafiya da mutane, musamman masunta.
Dagacin Yamman ya tuna cewa, lalle a 1982 Gwamnan Jihar Neja a lokacin, wato Alhaji Auwal Ibrahim, Sarkin Suleja na yanzu, shi ya bada umarnin a yi rusau a Gauraka, kusa da Tafa saboda kaurin sunan da ta yi. A lokacin, har sun giggina muhallansu a Tafa, bayan sun share filaye daga cikin dajin. Kawai sai wadanda rusau din ta shafa– Karuwai, ‘yandaudu, da masu shaye-shaye,suka kutsa kai cikin Tafa, kamar yadda Malam Shehu ya bayyana.
Ya kara da cewa, ita babbar hanyarAbuja zuwa Kaduna har Kano, kamfanin Dumed ne Suka fara ginawa a 1975, kuma aka kammala a 1980, amma kafin nan babu titi, sai hanya ta turbaya kawai. Sai ya shawarci al’ummar Tafa da su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya.
Shi ma Sakataren Defon Tirela na Tafa, Haladu Musa Usman cewa ya yi mutane ba su san cewa, a yau Tafa ta zama wuri mai tsarki ba da aka ci gaba, yana mai cewa, “yau a Tafa addinin Musulunci da na Kirista sun share duk aikin assha.”