Manoma mata a Jihar Ebonyi, sun bukaci matakan gwamnati uku na kasar nan, da su zuba jari mai yawan gaske a fannin noma. Har ila yau, sun yi nuni da cewa; hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalar karancin abinci a fadin kasar.
Manoman sun kara da cewa, kara samun zuba jari a fannin zai kara yawan tattalin arzikin noma zuwa a kalla kashi shida cikin dari.
Sun sanar da haka ne, a taron masu ruwa da tsaki kan kasafin kudi da jihar ta Ebonyi ta ware wa fannin a 2025.
An gudanar da taron ne, bisa hadakar ma’aikatar aikin noma da kula da albarkatun kasa ta jihar da kuma kwamitin kasafin kudi na jihar tare da kungiyoyin mata na kananan manoma.
Kana, an samu nasarar aiwatar da taron ne tare da goyon bayan kungiyar ‘Actionaid’; wadda ke gudanar da ayyukanta a Nijeriya.
Bugu da kari, manoman sun kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da tsare-tsare tare da kafa dokoki a kan yin amfani da magungunan kashe kwari da ke dauke da sinadaran da za su iya shafar kiwon lafiyar manoma.
Kazalika, sun yi kira ga majalisar dokokin jihar da ta tabbatar da an amince da kasafin kudin a kan lokaci da kuma yin amfani da dabarun kara bunkasa noma a jihar.
A cewarsu, yin hakan a kan lokaci; zai taimaka wajen rage yunwa da fatara, musamman don cika yarjejeniyar Maputo/Malabo da aka rattabawa hannu.
Sannan kuma, sun bukaci ‘yan majalisar da su tabbatar da cewa, sun mayar da hankali a fannin aikin noman; domin amfanin al’ummar mazabunsu.
Manoman, sun kuma shawarci ma’aikatar aikin noma ta jihar da hukumomin gwamnatin jihar, da su tabbatar sun fadada tuntuba da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma a yayin wanzar da kasafin kudin na badi.
Sun kuma bukaci a zuba jari na musamman, wajen sama wa manoma mata rance da kuma kayan aikin noma na zamani, musamman don rage yawan asarar da manoman ke yi.