ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Shekarar 2024: Mallam Umar A. Namadi

by Leadership Hausa
2 years ago
Namadi

Mallam Umar Namadi, Gwamnan Jihar Jigawa, ya samu lambar yabo ta LEADERSHIP ta Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2024, saboda irin kyakkyawan jagorancinsa wanda ya haɗa da gudanar da mulki mai cike da gaskiya da riƙon amana da samar da ababen more rayuwa da inganta tattalin arziƙi da kuma tallafawa jama’arsa a ɓangarori da dama na rayuwa.

Samun wannan yabo ya nuna yadda jagorancinsa ya haifar da sakamako da ci gaba mai ɗorewa wajen inganta rayuwar al’ummarsa.

  • Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati 2024: Shugaban Kwastam, Alh. Bashir Adewale Adeniyi
  • Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters

Tarihi Da Karatunsa

ADVERTISEMENT

An haifi Umar Namadi a garin Kafin-Hausa da ke jihar Jigawa, Allah ya albarkaci gidan da ya fito da ilimin addini. Kakansa shi ne Babban Limamin Kafin-Hausa, wanda ya kafa harsashin kyakkyawan jagoranci da sadaukarwa a rayuwarsa. Namadi ya fara karatunsa na firamare a Kafin-Hausa Central Primary School, sannan ya ci gaba a Mallam Madori Teachers’ College, inda ya samu takardar Teachers Grade II Certificate a shekarar 1982.

Bayan haka, Namadi ya rubuta jarrabawar A-Level a 1984, nasarorin da ya samu a fannin ilimi sun ba shi damar shiga Jami’ar Bayero ta Kano, inda ya kammala digiri a ɓangaren Akanta a 1987. Daga baya ya sake samun digiri na biyu a fannin Tsare-tsaren Kasuwanci (Business Administration) (MBA). Kazalika, Namadi mamba ne na ƙungiyoyin ƙwararru Akantoci da suka haɗa da; Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN), da Nigerian Institute of Management, da kuma Chartered Institute of Taxation.

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

Ƙwarewa a Fannin Kuɗi da Kasuwanci

Namadi ya yi aiki a fannonin kuɗi da masana’antu, inda ya fara aikinsa a matsayin babban jami’i mai kula da ƙananan bankuna (Principal Inspection Officer a National Board for Community Banks). Daga nan, ya yi aiki a Kaduna Textiles Limited da kuma rukunin kamfanonin Dangote, inda ya riƙe matsayi daban-daban, har ya zama jami’i mai kula da kuɗi (Financial Controller na Dangote Sugar Refinery) da sauran sassa na rukunin kamfanin Dangote.

Bayan haka, Namadi ya shiga harkokin kasuwanci na kansa, inda ya kafa kamfanonin Ɗanmoɗi Foods Processing Limited da Danmodi Farms Limited. Danmodi Foods ya zama masana’antar sarrafa shinkafa ta farko mai zaman kanta a Jihar Jigawa, wanda ya samar da ayyukan yi da dama ga matasa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Shigarsa Siyasa

Namadi ya fara siyasa ne a shekarar 2015 lokacin da ya zama kwamishinan harkokin kuɗi da tsare-tsare na Jihar Jigawa. A wannan matsayi, ya kawo sauye-sauye masu muhimmanci kamar aiwatar da tsarin asusun bai ɗaya (Treasury Single Account (TSA), wanda ya tabbatar da gaskiya da inganci a sarrafa kuɗaɗen jihar. Hakanan, shi ne ya fara tsara takardun kuɗaɗen jihar daga cikin gida, ba tare da dogaro da kamfanoni na waje ba.

Daga 2019 zuwa 2023, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, inda ya kasance ginshiƙi kuma abin koyi wajen riƙon gaskiya da amana. Wannan ya tabbatar da karɓuwarsa da amincewar jama’a har aka zaɓe shi a matsayin gwamna a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Jagoranci a Matsayin Gwamna

A matsayinsa na gwamna, Namadi yana jagorantar jihar bisa hangen nesa, inda ya fi mayar da hankali kan ayyukan more rayuwa da walwalar ma’aikata da noma da ilimi. Gwamna Namadi ya gina hanyoyi da gadoji da dama a faɗin jihar don haɗa yankunan karkara da birane. Wannan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙi da rage cunkoso a wuraren kasuwanci.

Noma: Ya tallafa wa manoma ta hanyar samar da taki mai rahusa da kayan aikin gona da bayar da horo kan sababbin fasahohin noma. Wannan ya ƙara samar da abinci da ayyukan yi ga matasa a jihar.

Ilimi: Namadi ya tabbatar da gyaran makarantu da ɗaukar malamai don inganta tsarin karatu. Hakanan ya kafa Gidauniyar tallafawa ilimi (Educational Foundation) tare da ƙanin sa, Dr Abdullahi Namadi, don tallafa wa ilimin yara.

Tallafi ga Jama’a

Namadi ya kasance gwarzo wajen tallafawa matasa da mata ta hanyoyin samar da jari da damar samun bashi mara kuɗin ruwa. Wannan ya bai wa matasa damar kafa sana’o’in dogaro da kansu, wanda hakan ya rage zaman kashe wando da kuma bunƙasa tattalin arziƙin gida.

Salon Jagoranci:

Namadi ya shahara da mutunci, da kula da jama’a kai tsaye. Ya kasance shugaba mai gaskiya da aiki tuƙuru, wanda hakan ya sa ake ganin sa a matsayin jagora abin koyi.

Tasiri Mai Dorewa

A gwamnatinsa ya tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a jihar Jigawa. A yau, jihar Jigawa tana kan tafarki mai kyau na ci gaba, inda Namadi ya gina kyakkyawan yanayi da samar da dama ga matasa da al’ummar jihar baki ɗaya. Wannan lambar yabo ta Gwamnan Shekara tana nuna yadda Namadi ya kasance jagora mai hangen nesa da kyakkyawan shugabanci.

Namadi
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22
  • Leadership Hausa
    Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa
Manyan Labarai

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Next Post
Gwarzon Shekarar 2024: Barr. Nyesom Ezenwo Wike

Gwarzon Shekarar 2024: Barr. Nyesom Ezenwo Wike

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

July 10, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026
CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

CMG Ya Gabatar Da Shiri Na Musamman Mai Taken “Samun Nasara Dangane Da AI+” A Ketare

July 10, 2026
Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

Zargin Da Wasu Sassa Ke Yiwa Kasar Sin Na Takure Sauran Kasashe Masu Tasowa Ba Shi da Tushe Ko Makama

July 10, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci

July 10, 2026
An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

An Ceto Dukkanin Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Jihar Oyo — Fadar Shugaban Ƙasa

July 10, 2026
Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

Xi Ya Zanta Da Shugabar Namibia

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.