Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
Wannan matsalar tana faruwa ne sakamakon toshewar wasu bututu daga cikin gabanta, kuma suna toshewa ne bisa sababi na rauni dake faruwa wajen haihuwa ko bari, sannan shedanun aljannu musamman jinnul Ashik na iya haddasa wannan matsalar, sannan shigar iska cikin gaba ma yana da tasiri wajen faruwar wannan matsala.
Idan gaban mace ya guntsi iska to ko yaya ta motsa iskar sai ta yi kokarin hurowa waje, don haka ne ma in aka sadu da ita sai iskar ta huro zuwa waje don haka sai iskar ta horo maniyyin waje.
Mafita:
Ta dinga motsa jiki nau’in gwale-gwale (wato a turance Skuatting ta bubbude kafafunta a tsaye tana yin sama tana mikewa tana tsugunawa a tsaye amma ta dinga yin kamar sau ashirin da safe ashirin da yamma, kuma ta dinga yin sit-up shima wannan adadin.
Sannan ta hada kanumfari da ‘ya’yan hulba, da tafarnuwa, da ganyen magarya tana dafawa tana shiga ciki, in ta bi wadannan hanyoyin in sha Allahu maniyyin zai zauna a cikinta ba zai dinga fita ba .
Sannan ta samu ganyan darbejiya wasu suna kiransa da maina wasu kuma da carbi to duk de wanda kuke kira shi nake nufi, sai ki sa a ciro miki ki wanke shi sosai da dan gishiri sai ki tafasa shi sannan ki bar shi ya sha iska haka daidai yadda za ki iya shiga, amma kar ki bar shi ya huce ko kuma ki ce za ki sairka shi da ruwan san yi a’a ba’a sa masa ruwan san yi sai dai ki barshi ya sha iska, ki zauna a ciki kamar tsawon minti 20-30 haka, za ki rika yi kamar a sati sau biyu haka. Ki yi kamar na tsawon wata daya zuwa biyu haka .
Ko kuma ki hada ganyen magarya da bagaruwa da lallai ki tafasa ki dan zuba gishiri kadan haka ki rika zama shima kamar tsawon minti 20 zuwa 30 haka. Za ki iya yi kullum ko safe da yamma za ki iya yi.