Karamar minista mai lura da harkokin lardi da sauye-sauye a lardin Mashonaland East dake kasar Zimbabwe, Apollonia Munzverengwi, ta ce hadin gwiwar Zimbabwe da Sin a fannin raya kwarewar ma’aikata, na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kyankyasar tarin kwararru mamallaka sana’o’i.
Jami’ar ta bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin liyafar da aka shirya a ofishin jakadancin Sin dake birnin Harare, fadar mulkin Zimbabwe, albarkacin shirin hadin gwiwar sassan biyu a fannin raya kwarewar ma’aikata. Ta ce, hadin gwiwar sassan biyu a wannan fanni, ya kuma karfafa kyakkyawar alakar dake tsakaninsu.
Munzverengwi ta kara da cewa, ta halarci taron karawa juna sani na ministoci, don gane da raya aikin gona na dijital, da farfado da yankunan karkara na kasar Sin, wanda karkashinsa tawagar Zimbabwe mai kunshe da jami’an gwamnati daga sassa daban daban, suka koyi wasu darussa game da ci gaban kasar Sin a fannin raya karkara ta hanyar farfado da kauyuka.
Kaza lika, jami’ar ta ce, sun koyi abubuwa da dama, sun kuma kuduri aniyar aiwatar da wasu dabaru da suka samo, wadanda za su taimaka wajen rage gibi tsakanin mawadata da talakawan Zimbabwe. (Saminu Alhassan)