Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya ce, gwamnatin tarayya tana bukatar karin wasu basukan kudade domin ta cike gibin kasafin kudinta, duk kuwa da cewa wasu ma’aikatu da rassa da sashi-sashi sun inganta harsashen hanyoyin shigar kudinsu.
Ministan ya shaida hakan ne yayin ganawa da hadakar kwamitin majalisar dattawa na kudin da na tsare-tsaren harkokin tattalin arziki kan tsarin kashe kudade na 2025 zuwa 2027.
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
- Karancin Takardar Kudi: Masu POS Da Bankuna Na Wasa Da Hankulan Jama’a
Edun ya ce akwai bukatar cikin basukan muddin majalisar dattawa ta amince da hakan.
“Yunkurin da ake yi kan kudin shiga yana tafiya daidai, amma akwai bukatar a kara himma, muna bukatar karin basuka masu albarka, inganci da dourewa.
“Ba kawai don gine-gine da manyan ayyukan ba, har ma don ayyukan jin dadi da walwalar jama’a, ayyukan kiwon lafiya, ilimi da ayyuka a fannonin kiyaye tsaron jama’a don taimaka wa masu karamin karfi da masu fama da talauci,” Edun ya shaida.
A nasa bangaren, ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu ya tunatar da ‘yan majalisar yunkurin ciwo bashi tiriliyan 35.5 a kasafin 2024, da farko an yi nufin sanar da gibin tiriliyan 9.7.
“Duk da tsare-tsaren kudaden shiga ya zarta na wasu hukumomin samar da kudaden shiga, har yanzu akwai bukatar gwamnati ta karbo rancen kudade don gudanar da kasafin kudin yadda ya kamata, musamman ta fuskar rabe-rabe da samar da ayyukan yi ga marasa galihu.
“Muna da tsarin hangen nesa na ci gaba na dogon lokaci na 2050,” in ji Bagudu.
Kazalika, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya shaida wa kwamitin cewa hukumarsa ta kwato sama da naira biliyan 197 daga watan Janairun 2024,
Ya lura cewa idan gwamnati ta yi aiki tukuru kuma ta samu tarin abubuwan da ake bukata, kasar za ta samu isassun kudaden da za ta kashe a kasafin kudin.
Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adeniyi, a cikin jawabinsa, ya bayyana cewa hukumar ta kwastam ta tara naira tiriliyan 5.352 na kudaden shiga fiye da naira tiriliyan 5.09 da aka yi niyyar yi a kasafin kudin shekarar 2024.
Ya ci gaba da cewa, naira tiriliyan 6.3 an yi niyya ne a matsayin kudaden shiga da aka yi hasashen za a samu a shekarar 2025, wanda kasha 10 daga ciki zai kasance abin da ake sa ran samun kudaden shiga a shekarar 2026 da karin kashi 10 na kasafin kudin shekarar 2027.
A nasa jawabin, babban jami’in gudanarwa na rukunin kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce kamfanin ya zarce kudaden shiga na naira tiriliyan 12.3 da aka yi hasashen za a iya samu a shekarar 2024, inda ya riga ya tara naira tiriliyan 13.1.
Har ila yau, shugaban hukumar tara haraji ta kasa FIRS, Zacch Adedeji, a nasa jawabin, ya sanar da kwamitocin hadin gwiwa cewa FIRS ta zarce kudaden shiga da aka yi niyya a sassa daban-daban na haraji.