Hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano, KIRS, ta kaddamar da cibiyar bayar da lasisin motoci ta tafi-da-gidanka da za ta rika shiga lungu da sako domin bunkasa tara kudaden shiga na jihar da kuma saukaka wa masu ababen hawa nauyin da ya rataya a kansu.
Da yake jawabi a wajen bikin ranar hukumar KIRS a yayin kaddamar da bikin baje kolin kasuwar duniya a Kano karo na 45, shugaban hukumar KIRS, Dakta Zaid Abubakar, ya bayyana cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu wajen inganta shirin samar da kudaden shiga na jihar Kano, don haka, aka samar da hikimar wannan shirin wanda zai taimaka wajen bunkasa kudaden shiga na cikin gida (IGR).
- Gwamna Yusuf Ya Mika Motocin Bas Na CNG Guda 10 Ga Kungiyar NLC Reshen Kano
- Hadin Gwiwar Zimbabwe Da Sin A Fannin Horas Da Ma’aikata Na Haifar Da Kyankyasar Tarin Masu Basira
“Wannan hikimar, ita ce irinta ta farko a Nijeriya, wato jihar Kano ce ta fara kaddamar da irin wannan yunkuri wanda za a rika yin rijistar motoci a ko’ina kuma a kowane lokaci ta hanyar amfani da fasahar zamani”. in ji shi.
A nasa jawabin, babban daraktan Hukumar KIRS, Malam Muhammad Abba Aliyu ya ce, matakin da hukumar ta dauka wani mataki ne mai mahimmanci da inganci wajen samar da kudaden shiga.
Ya bayyana cewa, a yanzu haka, hukumar ta kaddamar da cibiyoyin tafi-da-gidanka guda biyu kuma nan ba da dadewa, wasu za su biyo baya, inda ya bukaci sauran jihohi da su yi koyi da jihar Kano.