Saon kocin Manchester United Ruben Amorim ya samu nasarar farko a gasar Firimiya Lig yayinda Manchester United ta doke Everton da ci 4-0 a Old Trafford.
Rashford ne ya fara jefawa Manchester kwallo a minti na 34, minti 5 tsakani kuma Joshua Zirkzee ya jefawa Man Utd kwallo ta biyu ana dav da zuwa hutun rabin lokaci.
- Yau Za’a Kece Raini Tsakanin Manchester United Da Chelsea A Old Trafford
- Ana Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Bace Bayan Kifewar Jirgin Ruwa A Masar
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Manchester ta cigaba da jan zarenta a wasan yayinda Rashford da Zirkzee kowanensu ya sake jefa kwallo daya.
Da wannan sakamakon ne ta koma matsayi na 19 a teburin gasar Firimiya da maki 19 a wasanni 13 da ta buga,Amorim ya zama kocin Manchester United bayan ta raba gari da Eric Ten Hag wanda ya jagoranci kungiyar tsawon kakar wasa biyu.