Kocin Manchester City Pep Joseph Guardiola ya jagoranci wasanni 7 a jere ba tareda ya samu nasara ba a karon farko a tarihin aikinsa na koci tsawon shekaru.
A shekara 17 da ya shafe ya na aikin horar da kungiyoyi wannan ne karon farko da dan kasar Spain din ya jagoranci wannan adadin wasanni a jere ba tareda ya samu nasara a daya daga cikinsu ba.
- Ana Ci Gaba Da Neman Wadanda Suka Bace Bayan Kifewar Jirgin Ruwa A Masar
- City Za Ta Dawo Cikin Hayyacinta Duk Da Rashin Katabus Da Ta Ke Fama Da Shi – Pep Guardiola
Manchester City na cigaba da fama a wannan kakar bayan Liverpool ta doke ta da ci 2-0 a filin wasa na Anfield dake Liverpool a wasan mako na 13 a gasar Firimiya ta bana.