Majalsar dokokin ta jihar Zamfara ta zartar da dokar jin dadin al’uma da bayar da kariya ga mutane masu fama duk wani nau’i na nakasa a fadin Jihar.
Majalisar ta kuma bukaci a gaggauta kafa hukumar kula da harkokin nakasassu a fadin jihar.
- Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara
- Za Mu Ceto Zamfara, In Ji Atiku Yayin Da Ya Amshi Baƙuncin Dauda Lawal
Bayanin haka na kunshe a wata takarda da aka rabawa manema labarai da jami’in watsa labarai na majalisar, Mista Nasiru Biyabiki, ya sanya wa hanu.
Majalisar ta amince da dokar ne bayan da kwamitin kula da harkokin mata da yara kanana na majalisar ya gabatar da rahotonsa aka kuma yi zama a kansa.
Shugabanin kwamitin sun hada da Kabiru Magaji da Nasir Bello Lawal wanda suka gabatarwa da majalisar rahoton kwamitin don neman amincewarta.
An bayyana cewa, dokokin zasu taimaka wa gwamnati wajen yin maganin mastalolin da nakasassu ke fusakanta a fadin jihar.
Za a mika daftarin dokar ga gwamna, Bello Matawalle, don ya sanya hannu da zarar an kammala ayyukan da ya kamata kan dokar.