A yau Talata ne Shugaba Xi Jinping ya sake tabbatar da dukufar da kasar Sin ta yi wajen bunkasa magungunan gargajiya domin amfanar da al’ummar sassan duniya yadda ya kamata.
Ya bayyana haka ne a wasikar taya murna da ya aike wa Babban Taron Magunguna da Likitancin Gargajiya na Duniya na 2024 wanda aka bude a birnin Beijing a yau.
- Shawarar BRI Na Samar Da Wani Yanayi Mai Yakini Ga Tattalin Arzikin Duniya
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace Wasu A Sakkwato
Xi ya bayyana cewa ana bukatar karin kokari daga dukkan bangarori wajen karfafa hadin gwiwa a fannin likitanci da sauran harkokin kiwon lafiya domin a hadu tare a magance dimbin kalubalen kiwon lafiya da gina al’umma mai cike da lafiya ga kowa.
Shugaba Xi ya kara da cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki da sauran kasashen duniya domin ganin an karfafa fahimta da koyon ilimin juna a fannin magungunan gargajiya da kara shigar da su cikin tsarin kiwon lafiyar duniya da kuma habaka sabbin sauye-sauye da daukaka ci gaban magunguna da likitancin gargajiya.
Da ya juya ga batun tsarin Likitanci da Magungunan Gargajiya na Sinawa kuwa, Xi ya ce a ko yaushe kasar Sin tana bai wa fannin likitancin zamani da na magungunan gargajiya muhimmanci daidai-wa-daida kuma ta bunkasa hanyoyin ciyar da magungunan gargajiyar gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere).