Wani abun al’ajabi ya wakana a Abuja, inda wani boka mai suna, Ismail Usman, ya harbe kansa da kansa a cikinsa, yayin da ke gwada layar kariya daga harbin bindiga da ya hada da kansa.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Nuwamba a kauyen Kuchibuyi da ke Kubwa. A halin yanzu Bokan na kwance a asibiti rai a hannun Allah.
- Philippines Ta Sake Tada Rikici a Tekun Kudancin Sin Don Cimma Moriyarta
- Allah Ya Yi Wa Mawaƙin Kannywood, El-Mu’az Birniwa Rasuwa
A cewar ‘yansanda, Usman wanda malamin tsubbu ne ya yi sanadin halin da yake ciki yanzu sa’ilin da ya yi kokarin gwajin layar da ya hada, lamarin da ya juya har bindigar ta masa mummunar illa biyo bayan gaza yin amfani da layar da ta yi.
An yi gaggawar kwasan bokan zuwa babban asibitin Kubwa domin kokarin ceto rayuwarsa daga baya kuma aka sake maida shi zuwa asibitin kwararru ta Gwagwalada sakamakon tsananin da jikin nasa ya yi.
‘Yansanda dai sun yi gaggawar kai dauki ne bayan da suka samu kiran waya daga wani Shandam Michael, bayan da ya riski Boka Usman cikin mawuyacin hali. Lamarin da ya bai wa ‘yansanda damar zuwa har su kaisa zuwa asibiti.
‘Yansandan sun kwaso bindiga kirar gida da bokan ya yi amfani da ita da kuma layukan tsubbun da ya hada da sunan maganin harbin bindiga.
Sanarwar da ‘yansanda suka fitar sun ce, yanzu haka ana jinyar bokan da zarar ya warke kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba da kokarin hallaka kansa bisa dogara da sashi na 231 na Final Kot ta Arewacin Nijeriya.