Tun daga ranar 1 ga wannan watan da muke ciki ne kasar Sin ta soke harajin kwastam a kan dukkanin kayayyakin da take shigowa daga kasashen da suka fi fama da rashin ci gaba, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da ita a hukumance, ciki har da wasu kasashe 33 dake nahiyar Afirka. Hakan ya sanya ta zama kasa mai tasowa ta farko a duniya da ta dauki irin wannan mataki. A game da hakan, Dennis Munene Mwaniki, darektan zartaswa na sashen kula da harkokin Sin da Afirka karkashin cibiyar nazarin manufofin Afirka da ke kasar Kenya, ya ce, matakin da kasar Sin ta dauka na soke haraji zai taimakawa kasashe masu tasowa na fadin duniya wajen saukaka fatara da kuma gaggauta zamanintar da kansu.
Kasancewarta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tana sane da cewa, tabbatar da ci gaba shi ne ainihin matakin da zai taimaka wajen warware dukkanin matsaloli masu nasaba da talauci. Don haka, kasar Sin na ganin cewa, dole ne a tabbatar da bunkasuwar kasashen da suka fi fama da rashin ci gaba, a maimakon samar musu da taimako kawai.
- Kebbi Da Brazil Zasu Yi Haɗin Gwuiwa Kan Sarrafa Nama Ta Hanyar Zamani
- Kasar Sin Na Mai Da Hankali A Kan Halin Da Ake Ciki A Syria
Lallai, matakin da kasar Sin ta dauka a wannan karo na soke harajin kwastan, ya kasance mataki na tabbatar da bunkasuwar kasashen da suka fi fama da rashin ci gaba. Sanin kowa ne kasashen ba sa rasa kayayyaki masu inganci, sai dai sun kasa samun damar shiga kasuwannin duniya, wasu kuma sabo da yawan kudin da za su biya don fitar da kayayyakinsu zuwa ketare. Ga shi yanzu, yadda kasar Sin ta soke harajin kwastan ya samar da kyawawan sharudda ga kasashen da matakin ya shafa wajen fitar da kayayyakinsu masu inganci zuwa kasar Sin, kuma hakan tabbas zai sa kaimin bunkasuwar sana’o’in kasashen, tare da sa kaimi ga samar da guraben aikin yi da saukaka fatara. Muna iya hasashen cewa, bisa ga matakin, kayayyaki masu inganci na kasashen da suka fi fama da rashin ci gaba a Afirka, ciki har da abarba na Benin da gahawa na Habasha da tattasai na Rwanda da zuma na Tanzania, sai kuma naman rago na Madagarscar, za su gaggauta shiga babbar kasuwar kasar Sin, wanda hakan zai samar musu babbar damar tabbatar da ci gabansu.
Zamanintar da kansu buri daya ne ga Sin da kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa. A lokacin da take kokarin zamanintar da kanta, kasar Sin ba ta son ganin ita kadai ta cimma burinta, a maimakon haka, tana son ganin kowa burinsa ya cika. Don haka, a lokacin da take raya kanta, har kullum kasar Sin na dukufa a kan raba damammakinta ga kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa. Hakika, ban da matakin nan na soke harajin kwastan, ta kuma samar da kafar musamman ga kayayyakin amfanin gona da kasashen Afirka ke fitarwa zuwa gare ta, tare da samar da sauki ga kamfanonin kasashen Afirka wajen halartar bukukuwan baje kolin da ta shirya, irinsu bikin baje kolin kayayyaki da suke shigowa daga ketare, baya ga haka, ta kuma samar musu taimako wajen horar da kwararru, da dai sauransu.
A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a watan Satumban bana a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin cewa, ba za a bar kowace kasa a baya ba a kokarin da suke yi na zamanintar da kansu. Dukkanin kasashen Sin da Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa, sai mu hada karfi da karfe, domin cimma wannan burinmu na bai daya. (Lubabatu)