Babban Hafsan Sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana fatansa na cewa, nan ba da jimawa ba za a kawar da kungiyar Lakurawa, ta hanyar karfafa hadin gwiwa da kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya.
Oluyede ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Gwamnatin Kaduna Ta Gargaɗi Jami’anta Kan Rubutu A Kafafen Sadarwa
- Ba Laifi Ba Ne Seyi Tinubu Ya Nemi Takarar Gwamnan Jihar Legas – Ƙungiyar Matasa
Da yake jawabi a ziyarar tasa, Laftanar-Gen. Oluyede ya jaddada kudirinsa na inganta yanayin tsaro a Nijeriya, inda ya yi alkawarin samar da sabuwar hanyar magance matsalar rashin tsaro.
COAS ya kuma bayar da bayanai kan ziyarar da ya kai a sansanonin sojoji a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya bayyana cewa, ganawarsa da dakarun sojojin ta jaddada muhimmancin kawo karshen rashin tsaro a fadin kasar nan.