Rumfar kasar Sin a taron kasashe da suka kulla yarjejeniyar hana kwararar hamada ta MDD karo na 16 wato COP 16, ya gudanar da karamin taro a jiya Litinin, mai taken “Fasahar kiyaye muhalli da makoma mai kyau”, inda kasar Sin ta more dabarun samun ci gaban hadin gwiwarta da sauran kasashe a bangaren hana yaduwar hamada.
A yayin wannan taro, an gabatar da ci gaban gina lambun shan iska na kare muhalli tsakanin Sin da Afirka, wanda cibiyar nazarin halittu da yanayin kasa ta jihar Xinjiang, da kungiyar babbar ganuwar itatuwa ta Afirka suka yi hadin gwiwa wajen ginawa a Nouakchott, hedkwatar kasar Mauritaniya.
- Xi Jinping Ya Gana Da Manyan Jami’An Muhimman Kungiyoyin Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa
- Netanyahu Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Rashawa
Ban da wannan kuma, cibiyar ta ci gaba da fitar da takardar karawa juna sani da sashin ofishin sakataren kungiyar. Kaza lika, an gabatar da ci gaban da aka samu wajen dakile kwararar hamada bisa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, da tsakiyar Asiya da sauransu.
Darektan sashen hana kwararar hamada na hukumar sana’ar itatuwa, da filin ciyayi ta kasar Sin Huang Caiyi, ya gabatar da jawabi, inda ya ce Sin na fatan hadin gwiwa da mabambantan bangarori, don more dabararta, da fuskantar kalubaloli tare, da ma tattaunawa kan fitar da wata hanya da ta dace ta tinkarar yaduwar hamada, da manufofi mafiya dacewa da za a bi cikin hadin kai, ta yadda za a cimma burin gaggauta cin gajiyar hamada.
A nasa bangare, babban jami’in hukumar kare babbar ganuwar itatuwa ta Afirka a kasar Mauritaniya Sidna Ould Ahmed Ely, ya gabatar da jawabi dake bayyana shirin kirkire-kirkire da Sin ta gabatar, na taka rawar gani wajen goyon bayan kokarin da Mauritaniya ke gudanarwa wajen dakile kwararar hamada, da raya shirin babbar ganuwar itatuwa ta Afirka. (Amina Xu)