Sau da yawa mutane kan yi mamakin irin hikimomin kasar Sin mai al’umma kusan biliyan daya da rabi ke amfani da su, wajen gudanar da al’amuranta, saboda yadda wasu ke cewa “idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai”.
Bari mu zakulo wasu daga cikin hikimomin da kasar ke amfani da su daga jawaban da Shugaba Xi Jinping ya gabatar a wurare da lokuta daban-daban.
- Sarki Sanusi II Zai Sake Ayyana Wata Rana Ta Naɗa Sabon Hakimin Bichi
- Kwamitin Ɗanyen Mai Ya Nuna Rashin Gamsuwa Da Jinkirin Haƙo Mai A Kolmani
Ga misalin farko game da nuna tausayin al’ummarta da kula da halin da jama’a za su shiga a kowane irin mataki da gwamnatin kasar za ta dauka.
A taron tattaunawar da aka yi da wakilan ’yan kasuwa da masana ilimi a ranar 23 ga Mayun 2024, Shugaba Xi ya ce, “Kamata ya yi a dauki matakan gyare-gyaren da za su magance matsalolin da suka fi damun al’umma da kuma saurare da aiwatar da abin da suke so, sannan a dauki kwararan matakai da za su samar da fa’ida ta hakika ga jama’a, da samun amincewarsu da mutunta ra’ayoyinsu gwargwadon iko, ta yadda gyare-gyaren da ake yi za su tabbatar da cikar burinsu da faranta musu rai da ba su cikakken tsaro.”
Ina da yakinin duk wanda ya sa kafa a kasar Sin, zai ga abubuwan da shugaban ya ambata a aikace.
Har ila yau, a dai wannan taron da wakilan ’yan kasuwa da masana ilimi, shugaban ya ce, “Yana da matukar muhimmanci a bi abubuwa sau da kafa da kuma inganta tsarin tattalin arzikin kasarmu, da gina babban tsari na tafiyar da tattalin arzikin kasuwanci bisa turbar gurguzu, da inganta tsarin kula da kananan sana’o’i da hanyoyin samar da ci gaba mai inganci.”
A nan, za a fahimci irin yadda kasar Sin take bin tsare-tsaren kawo ci gaba,da kyautata yanayin kasuwanci, da nuna ishara ga masana ilimi a kan ba da gudummawa wajen bayar da shawarwari a kan kula da kananan sana’o’i, da kawo hanyoyin samar da ci gaba mai inganci.
Kamar an tambayi Shugaba Xi, to ta yaya kasar Sin take aiwatar da tsare-tsarenta cikin nasara? A jawabin da ya gabatar a zaman nazari na rukuni-rukuni da aka yi lokacin taron sashin siyasa na Kwamitin Tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis karo na 14, a ranar 27 ga Mayun 2024, ya ce, “Don magance matsalolin da suka shafi tsarin ayyukan yi da kawo ma’aikatan da ake bukatar a samar daidai da bukatu, ya kamata a yi kokarin hanzarta habaka samar da ma’aikata na zamani masu kwarewa da suka dace da zamani wadanda za su wadatar da kuma rarraba su a bisa ingantaccen tsari.”
Dangane da batun kimiyya da fasaha wanda duniya ke yi a zamanin nan, kasar Sin ta kasance jagora. Ga kuma daya daga cikin sirrukan kasar daga abin da Shugaba Xi ya ce a jawabinsa lokacin taron koli na kasa a kan kimiyya da fasaha da aka yi ranar 24 ga Yunin 2024, “Yana da matukar alfanu a sada tsakanin sabbin kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha da kuma ci gaban masana’antu, ta yadda hakan zai taimaka wajen samar da sabbin ginshakai na kawo ci gaba.”
A bangaren muhalli kuwa, a halin yanzu kowa ya san yadda ake tataburza a tsakanin kasashe masu tasowa da masu karfin tattalin arziki game da gurbata muhalli, ta wannan fuskar ma, kasar Sin tana ci gaba da daukar matakai a cikin gida da yekuwar hakan a waje. Shugaba Xi ya bayyana hikimar kasar Sin a taron koli na kasar a kan kiyaye lafiyar muhalli, da ya gudana ranar 19 ga Yunin 2023, inda ya ce, “Ya kamata babban matakin kare muhalli da ake dauka ya taimaka wa kasar Sin ta ci gaba da samar da sabbin turaku da hanyoyin raya kasa, da kara himma ga gina tattalin arziki mara gurbata muhalli. Ta haka kasar za ta yi tsimin kudin da take yawan kashewa da rage gurbata muhalli yadda ya kamata, sannan za ta ci gaba da karfafa kokarinta na dorad da ci gaba.”
Daga wadannan misalai daga jawaban Shugaba Xi, ana iya fahimtar yadda kasar Sin ke bai wa ko wane bangare hakkinsa domin samun dorewar ci gaba, ba kawai ga kanta ba har ma da duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)