Da akwai alamun jami’oi za su fara wani yajin aikin da za s a al’amuran koyarwa su tsaya, yayin da gwamnatin tarayya ta kasa cika alkawarin yarjejeniyar da ta sa hannu da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa (ASUU).
Jaridar Guardian ta bada rahoton cewa kungiyar ta damu kwarai kan rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi da ita, na samar da Naira bilyan 200 kowace shekara wanda aka yi 2009 kudaden da za bunkasa jami’oin Nijeriya.
- Sin Da Amurka Sun Tsawaita Yarjejeniyar Hadin Gwiwa A Fannin Raya Kimiyya Da Fasaha Da Karin Shekaru 5
- Bankin Duniya Da Hukumar Lamuni Ke Yi Wa Tsarin Ilimin Nijeriya Zagon-kasa – ASUU
Babban jami’in kungiyar da baya son a ambaci sunansa, ya bayyana cewa kungiyar ta shiryawa tafiya yajin aikin, muddin dai gwamnati ta ki sakin kudin saboda ayyukan da ake yi masu muhimmanci da suke karkashin kungiyar, shirye suke su fara yajin aiki idan har Shugaban kasa bai sa an bada kudaden ba.
Wata majiya tace matakin na, ASUU da har yanzu ba’a bayyana shi ba, ya tsaya kan rashin cika alkawarin da gwamnati ta yi na cika alkawarin da tayi tare da kungiyar a shekarar 2009 kan tsarin bukatunsu.Tsarin da aka dauka a matsayin mai canza al’amura wajen sake farfadowa da bunkasa abubuwan more rayuwa da za su taimakawa bunkasar ilimi a Jami’oin Nijeriya.
Majiyar ta ce shi shirin tafiya yajin aikin da za a yi ya dogara ne kan samun matsaya wadda ake sa ran cimmawa bayan taron da za a yi na kwamitin zartarwa nan gaba bada dadewa ba.
A wani ci gaban da aka samu wani babban kusa, na cibiyar kulawa da ayyuka ta jami’ar Jos Dr. Tunde Olagunjembi, wanda shi ne babban mai bincike ne, daga Jami’ar har ila yau kuma Malamin, ya ba Shugaban kasa shawarar kada ya yi watsi da tsarin da aka fara wanda an yi shi ne, domin samar da kudade ga Jami’oin gwamnati saboda ci gabansu. Tsarin da aka fara an kirkiro shi ne domin a samu yin gyara kan abubuwan more rayuwa da suka lalace da kuma samar da kayan koyarwa a manyan makarantu.
Olagunjembi ya yi kira da Shugaban kasa ya ci gaba da tsarin da aka fara domin samun ci gaban yadda ake tafiyar da ilimin Jami’oi.
Ya yi kira da Shugaban kasa da kada ya bata lokaci ya amince saboda ci gaba na yin ayyukan, a makarantu da suke a karkashin tsarin.
Ya lashi takobin al’ummar Jami’a da kungiyar ASUU sun kosa da ganin yadda za a ci gaba da ayyukan a karkashin wannan mulkin.
Babban mai fada aji a Jami’a ya kara bayyana cewa samun dorewar karatu a makarantu hakan na faruwa ne sanadiyar sadaukar da kan da ‘yan kungiyar ta ASUU suka yi wadanda suka yanke shawarar za su ba Shugaban kasa lokaci domin ya samu damar tsai da hankalinsa kan ayyukan dake gabansa.
Sai dai kuma duk da hakan ya ja kunne cewar ruwa ya kusa karewa dan Kada,kamata ya yi Shugaban kasa ya dauki matakan da suka kamata wajen samar da kudade don ci gaban ayyukan da aka fara.
Kamar yadda yace gabatar da, fara amfani samar da kudade saboda a samu aiwatar da tsarin yin ayyuka, hakan ta yiyu ne saboda yarjejeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, abin ya ta’allaka ne saboda ayi amfani da shawarwarin kwamitin ya bayar, domin ayi maganin matsalolin da ake fuskanta a manyan makarantu/ Jami’oin Nijeriya.