Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai magana ne game da zargi da yake shiga tsakanin mutum biyu wadanda suka kusa aure.
Me ke kawo wannan zargi?
Fa’iza Musa
Abin da nake ganin yana kawo zargi shi ne, farko dai ni gaskiya ina ganin rashin sani addini da rashin sanin meye shi hukuncin zargin, domin in mutum ya san addini gwargwado da kuma hukuncin zargi da kuma hukuncin haramcin zargi a Musulunci zai yi duk abin da zai yi wajen kiyaye shi tun da kin ga kafin ka je ka ce kana son mutum ko Annabi ma ya fada mana cewa mu zabi me addini, cikin zamantakewarmu in mace ce ta zabi namijin mai addini shima kuma ya zabi mace mai addini daidai gwargwado domin zaman takewa na yau da kullum da kuma tarbiyyar ‘ya’ya, matukar ya zabi mai addini ko ta zabi mai addini tun kafin aure zai zamanto akwai takaitatcan zargi a tsakaninsu koma a ce ya zamanto babu zargin, saboda in na yarda dake na yarda da addininki na yarda da imaninki ba zai zamanto ina zarginki akan kome ba tun da gwargwado zan yi tunanin kina tsoran Allah duk abin da za ka yi kana yin sa domin Allah kuma duk abin da zaka yi ba za ka yi shi don ka cutar da wani ko ka cutar da kanka ba.
- An Kori Tsohon Manajan Banki Bisa Zargin Damfarar Naira Miliyan 122
- Netanyahu Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Rashawa
Sannan na biyu ko na uku abin da yake kara janyo tsargi tsakanin ma’aurata shi ne karya, su sa karya a cikin lamarinsu su zamanto makaryata don yana ganin sai ya yi karya za ta so shi, ko kuma ita ta zamanto makaryaciya ko wani abin ko kuma mai son abin duniya ko wani abin shima wannan ya kan iya jawo zargi ko wani abin saboda zai rinka ganin kamar ta raina abin da yake da shi, kila hankalinta ba a kanshi kadai yake ba.
Sannan na uku kuma shi ne, yawan mu’amala da mutane da yawa, ya zamanto in kina tare da namiji ki ga yana mu’amala da mutane da yawa wato jinsin da ba nashi ba da yawa ko kuna tare ko kuna hira ko wani abu, ya zamanto kuna tare da shi yana yawon mu’amala da mata ko wani abu haka wanda de suke a tsammaninki ba muharramansa ba shima wannan yana kawo zargi to ya kamata duk wadanda za su yi aure a tsakanin mace da namiji koda a ce suna mu’amala da wasu daban a wajen jinsin daba nasu ba ya kasance duk lokacin da suke tare su kan dan takaitawa saboda kin ga wani namijin dan kasuwa ne ba yadda za’a yi a ce ba zai yi mu’amala da mata ba to lokacin da yake mu’amala da matan ya kasance ya sanar da ita da suwa yake yi ko kuma ma ya takaita lokacin ya rinka samun wani lokaci na kasuwancinshi shi da kuma lokaci na ita wacce zai aura koda bai aure ta ba shima a ganina in ya zamanto koda yaushe ne sai suna tare ko ita tana kasuwanci ko ita ma’aikaciyace tana mu’amala da maza yakasance duk lokacin da za ta yi lokacin wanda za ta aura daban lokacin da za ta yi mu’amala da abokan kasuwancinta daban.
Sai kuma shine abin da nake ganin yafi kome ma kawo zargi shi ne ma’aurata dayansu ya zamo mai magana da batsa duk maganar da za su yi tsakanin shi da wacce zai aura kai koda bayan ya aure ta ne ya zamanto da kamun kai sannan ya zamo yana furta maganganu daba za su zubar masa da mutunci ba, maganar data halatta maganar da ta zamto ba ta sabawa shari’ar Muslunci ba, wani lokaci za ki ga ma’auratanmu musamman samari da ‘yan mata wadanda kansu yake fuzga za ki ga don ina ganin za ka aure ni ko za ki aureni ina da damar in miki kowace irin magana to za ki ga saboda ina ganin kamar muna da kusanci wannan kuma ba daidai bane tsakanin ma’aurata wanda za su yi aure kai koda kun yi aure, akwai kalmomin da ya kamata mutum ya rinka furtawa mutum ba sai ya furta ba saboda su kan iya zubar misa da mutumci sannan kuma su kan iya sa zargi a tsakaninsu ya zamanto duk kalmar da za ka furta kalma ce mai kyau wanda shari’a ta yarda da shi sannan kuma magana ce wanda kunne zai dauka ba batsa bane ba, wanda ko a Musulunci haramun ne . Allah ya sa mu dace.
Bilkisu Maharazu
Abin da ke kawo zargi tsakanin wadanda suke gab da sun yi aure shi ne: Na farko akwai zafin kishi wanda shi wannan zafin kishin idan ya yi yawa shi ne yake kawo zargi tsanin ma’aurata har ya kan kai da rabuwa a tsakanin su kwata-kwata, saboda idan ya yi yawa sai ki ga kullum ana ta fadace-fadace a tsakaninsu.
Na biyu akwai rashin fahimta juna saboda ba a yi auren aka zauna ba ballantana a fahimci juna, amma ya kamata ku kasance masu fahimta juna, tun kafin ku yi aure, to da zarar an fahimci juna, to sai komai ya tafi daidai yadda ya kamata, ba tare da an samu matsala ba, sai dai dan abin da ba za a rasa ba, na yau da kullum wanda dama shi aure haka yake ga kowa, masu magana na cewa zo mu zauna zo mu saba. Muna fatan alkhairi da duk masu shirin yin aure da wadanda suke ciki Allah ya zaunar da su lafiya.
Usman Sani
Haka na iya faruwa ne, saboda rashin fahimtar juna, rashin amincewa, ko kuma yayin da aka samu maganganun banza daga wasu mutane ko ‘yan uwa.
Saboda wasu za ku ga ana samun yawan gulmace-gulmace na mutane na kai kawo a tsakaninsu, sannan akwai shedan wanda dama shi ne ummul haba’isu, shike haddasa komai, shike sawa mutum wasuwasi yanzu haka wani na can yana yin kaza, shi ne ya hada ku ya sa maka zargi, daga nan sai ka fara ganin laifin dan uwanka, kana ganin kamar yana can yana cin amanarka. Haka nan, idan akwai al’amar rashin gaskiya a cikin al’amuran daya daga cikin ma’auratan, hakan na iya haifar da zargi, saboda zai rika ganin kamar dayan ma haka yake, saboda shi ya sa ba gaskiya yake ba.
Abdurrahman Tijjani
Gaskiya ni a ganina, babban dalili shi ne, shedan, saboda dama shi shedan duk wani abin alkhairi da za’a yi kokarin yi shi, kuma sai ya yi iya bakin kokarinsa ya ga ya bata wannan abin. To wannan shi ne babban masabbabin abin da yake kawo zargi tsakanin ma’aurata ko kuma wadanda suke gab da yin aure.
Da zarar mutum bai yi kokarin fin karfin zuciyarsa ba to gaskiya shedan zai yi kokarin mamaye ta, da zarar ka bari shedan ya yi nasara a kanka to fa al’amuranka sai abin da hali ya yi saboda duk abin da zuciyarka ta raya, haka za ka ga shi ne daidai a wajenka koda ba daidai bane. Allah ya sa mu dace.
Khadija Abdullahi
Ni a ganina, gaskiya abin da ke kawo zargi tsakanin wadanda suke gab da aure shi ne, so ya yi yawa, to shi ne sai ka rika ganin kamar wanda kake so yana tare da wata, ko shi ya rinka ganin kamar ta tana tare da wani, su rinka ganin a junansu kamar daya yana cin amanar daya.
Sannan kuma dama, shedan ne ke kawo irin wadannan wasiwasin, shi ya sa ake so mutum ya yi kokari ya fi karfin zuciyarsa, saboda kar shedan ya mamaye masa zuciya.
Idan kana son mutum to ka sa yarda a tsakaninku, koda wasa kar ka yi kokarin kawo kukwanto a tsakaninku, to idan kuka yi haka za ku ga babu wani kokwanto da zai rika shiga tsakaninku. Allah ya sa mu dace.