A ranar Juma’a ne Sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya ajiye aikinsa bisa dalilan da ba su bayyana ga jama’a ba zuwa yanzu.
Sakataren ya ajiye aikin ne a wata wasiƙa da ya aike kai tsaye wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad.
- Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Watsi Da Ƙara A Kan LEADERSHIP
- Dabaru Da Fasahohin Sin Na Taimakawa Kasashen Afirka Wajen Tinkarar Kwararar Hamada
Tuni dai gwamna Bala Muhammad ya amince da ajiye aikin sakataren gwamnatin nasa tare da masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba.
Gwamnan a wata sanarwar da kakakinsa, Mukhtar Gidado ya fitar da yammacin ranar Juma’a, ya ce, ya amince da murabus ɗin Ibrahim Muhammad Kashim a matsayin SSG nan take.
Gwamnan ya umarci shugaban ma’aikatar fadar gwamnatin jihar, Dakta Aminu Hassan Gamawa da ya ci gaba da kula da harkokin ofishin SSG na riƙon ƙwarya kafin a naɗa sabo.
“A madadin gwamnatin jihar Bauchi da al’ummar jihar, ina matuƙar godiya ga Ibrahim Muhammad Kashim bisa hidimar da ya yi wajen ci gaban jihar Bauchi. Ina masa fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba,” a cewar sanarwar.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, har yanzu dai ba a san dalilan da suka sanya SSG ɗin ajiye muƙaminsa ba wanda ke zuwa bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar jihar da ya gudana a ranar Alhamis.