ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, In ji Ministan Yaɗa Labarai

by Sulaiman
12 months ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da cikakken goyon baya ga ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin ’yan jarida, tare da fahimtar muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen gina ƙasa.

Da yake jawabi a taron lacca na shekara-shekara na kamfanin jaridar Blueprint wanda aka gudanar a ranar Talata a Abuja, Idris ya ce tun farkon naɗin sa, Shugaba Tinubu ya bayyana masa cewa ya ba shi dama ya yi aikin sa yadda ya ga ya dace a matsayin sa na ƙwararre.

ADVERTISEMENT
  • Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi,  Jafaru Ilelah, Rasuwa
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babban mai goyon bayan kafafen yaɗa labarai ne. Yana da masaniyar cewa kafafen yaɗa labarai suna da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa, kuma ya sha gaya mini cewa in ci gaba da aiki na yadda na ga ya dace, kasancewa ta ƙwararre.”

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.”

Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma.

“A yayin da kuke yin wannan aiki, kuna da babban nauyi na riƙe gwamnati da shugabanni da alhakin aikin su. Amma ko da kuna yin hakan, dole ne ku sani cewa saboda matsayin ku na musamman da rawar da kuke takawa, za ku iya taimaka wa ƙasa matuƙa, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, ayyukan ku na iya cutar da al’umma,” inji shi.

Ya bayyana buƙatar sanin ya kamata da hankali wajen tantance sahihin bayani daga wanda zai iya ɓata zaman lafiya ko raba kan al’umma.

Ministan ya ce duk da ƙalubalen da ke fuskantar fannin yaɗa labarai, akwai haske a gaba domin kafafen sun ci gaba da nuna jajircewa da ɗorewa.

Ya kuma bayyana cewa ba shi ba ne Shugaban kamfanin jaridar Blueprint ba tun bayan da aka naɗa shi Minista.

“Ba ni ne shugaban jaridar Blueprint ba yanzu. Ni ma baƙo ne aka gayyata zuwa wannan taro. Na san cewa a baya ni ne ke gaba wajen shirya wannan taron na Blueprint, musamman tun lokacin da aka kafa ta shekaru 14 da suka wuce. Dole ne in gode wa waɗanda aka gayyata su haɗu da ni a watan Mayun 2005 domin tunanin fara jaridar Blueprint: Malam Ibrahim Sheme; Manajan Darakta, Malam Salisu Umar; Shugabar Kwamitin Tace Labarai, Hajiya Zainab Okino, da dukkan ma’aikatan jaridar Blueprint.

“Na gode da cigaba da tafiyar da abin da muka faro cikin nasara. Na shekara guda ban ziyarci ofishin ba, amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi hakan. Ina so in ga ko har yanzu kuna ci gaba da tafiyar da abin da muka faro. Ina alfahari kuma ina farin ciki da cewa abin da muka fara ya ci gaba da bunƙasa,” inji shi.

Idris ya taya waɗanda suka samu kyaututtuka murna, inda ya bayyana cewa ba a yi masu kyautar bisa wani son zuciya ko tasiri daga wani waje ba, sai hukuncin jaridar ne kaɗai.

Cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake; Ministan Raya Noman Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, da babban baƙon jawabi na taron, Farfesa Attahiru Jega.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Sulaiman
    Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin
  • Sulaiman
    Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni
  • Sulaiman
    ‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

MASU ALAKA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Labarai

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Labarai

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

July 10, 2026
Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
Labarai

Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

July 10, 2026
Next Post
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Makarantun Kano Za Su Fara Hutun Ƙarshen Zango A Ranar Juma'a - Gwamnati

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 10, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

July 10, 2026
Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu

July 10, 2026
Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Kan Gyaran Kudirin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Kan Gyaran Kudirin Dokar Shari’ar Manyan Laifuka

July 10, 2026
Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf

Taƙaddamar Kafa Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci A Yi Binciken Ƙwaƙwaf

July 10, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

Asusun IMF Ya Rage Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya, Ya Kuma Kara Na Sin

July 9, 2026
Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

Alkaluman Farashin Kayayyakin Masarufi Na Kasar Sin Sun Karu Da Kaso 1 A Watan Yuni

July 9, 2026
‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

‘Yansandan Jihohi Za Su Bai Wa Gwamnoni Cikakken Iko Wajen Yaƙi Da Matsalar Tsaro — Gwamna Dauda

July 9, 2026
Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum

Taron Intanet Na Sin Karo Na 25 Ya Bayyana Yadda Ake Amfani Da Fasahar AI A Rayuwar Yau Da Kullum

July 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.