Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba ta (CDD), ta yi Allah-wadai da cin tarar Naira miliyan biyar da Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta yi ga gidan talabijin na Trust TV da wasu kafafen yada labarai uku, saboda watsa shirye-shiryen da suka shafi ‘yan ta’adda.
Trust TV mallakin kamfanin Media Trust Group ne,kamfanin da ke buga jaridun Daily Trust, Aminiya da sauransu.
Haka nan NBC ta ci tarar kamfanin Multichoice Nigeria Limited, mamallakan DSTV, TelCom Satellite Limited (TSTV) da NTA-Startimes Limited, saboda watsa wani shiri da hukumar yada labarai ta BBC ta yi mai taken, ‘Bandits Warlords Of Zamfara’.
CDD, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar da Daraktarta, Idayat Hassan ta fitar, ta bayyana sanya tarar a matsayin abin zalunci, inda ta bukaci hukumar ta janye matakinta cikin gaggawa.
A cewar Hassan, tarar wani yunkuri ne na cin mutuncin kafafen yada labarai da kuma tauye hakkin ‘yan kasa na fadin albarkacin bakinsu da yada labarai.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun yin Allah wadai da kakkausar murya kan tarar da Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta yi ga gidan talabijin na Trust TV da sauran kafafen yada labarai.
“Mun yi mamakin daukar matakin ba tare da bai wa kafafen yada labaran da abin ya shafa lokaci ba don mayar da martani don kare kansu.
“A matsayinmu na abokan aikin gidan talabijin na Trust TV wajen shirya shirin, ba tare da neman afuwa ba mun jaddada cewa an yi shirin ne kuma an watsa shi ne domin amfanin jama’a. An gina shirin ne bisa tsawon shekaru da aka shafe ana gudanar da bincike a fagen, wanda ke wakiltar dukkanin al’ummomin da abin ya shafa da kuma samar da hanyoyin kawo karshen rikicin.
“Yayin da babban zaben 2023 ke karatowa, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta guji yin duk wani abu da zai kawo barazana ga harkar yada labarai ko kuma tauye ‘yancin fadin albarkacin baki da ‘yancin ‘yan kasa.”