Dakarun rundunar soji ta ‘Operation Fansan Yamma’ sun tarwatsa sansanoni 22 na ‘yan ta’addan Lakurawa tare da kashe su da dama a jihar Sakkwato.
Haka kuma sun kwato makamai da alburusai yayin harin.
Mukaddashin babban kwamandan runduna ta 8 kuma kwamandan sashi na 2 na rundunar Fansar yamma, Birgediya Janar Ibikunle Ajose ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake jawabi ga runduna ta musamman da aka tura domin murkushe Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi da babban hafsan sojin kasar ya tura a ranar Juma’a.
A cewarsa, tura karin rundunar ta musamman, zai kara wa rundunar da ke aiki a yankin karfin gwiwa da kuzari wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma baki daya.