Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sabbin naɗin muƙamai da sake naɗin wasu shugabannin hukomomi da masu ba da shawara na musamman. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, yau Lahadi.
Daga cikin sabbin waɗanda aka nada akwai Dr. Ibrahim Musa, sanannen masani a fannin kiwon lafiya daga Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), da kuma shahararren ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood, Sani Musa Danja.
- Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5
- Gobara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Magidanci Da Matarsa A Kano
Sabbin Naɗe Naɗen sune:
1. Dr. Ibrahim Musa – Mai ba da Shawara kan harkokin Lafiya
2. Dr. Hadiza Lawan Ahmad – Mai ba da shawara kan fannin zuba jari
3. Sani Musa Danja – Mai ba da Shawara a harkokin Matasa da Wasanni
4. Barr. Aminu Hussain – Mai ba da Shawara kan harkokin Shari’a
5. Dr. Ismail Lawan Suleiman – Mai ba da Shawara a fannin lura da yawan jama’a.
6. Nasiru Isa Jarma – Mai ba da Shawara kan ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs)
7. Hon. Wada Ibrahim Daho – Kwamishinan SUBEB
8. Hon. Ado Danjummai Wudil – Sakataren hukumar bayar da shawara da sanya mutane a turba.
9. Dr. Binta Abubakar – Sakataren Zartarwa a hukumar ilimin manya.
10. Hon. Abubakar Ahmad Bichi – Daraktan Janar, ƙananan sana’o’i da ƴan talla.
11. Hon. Abdullahi Yaryasa – Mamba a hukumar lura da majalisar dokoki.
12. Dr. Yusuf Ya’u Gambo – Shugaba, fannin tsare-tsaren dokoki da manufar gwamnati.
Sake Naɗin Jami’an Gwamnati:
1. Hon. Kabiru Getso Haruna – Sakataren Zartarwa a hukumar bayar da tallafin Karatu.
2. Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo – Sakataren Zartarwa, KSSSSMB
3. Dr. Kabiru Ado Zakirai – Sakataren Zartarwa a fannin ɗakunan karatu (Library)State Library Board)
4. Dr. Abubakar Musa Yakubu – Daraktan Lafiya a Asibitin gidan Gwamnati
5. Yusuf Jibrin Oyoyo – Mai ba da Shawara kan harkokin ɗalibai
6. Hon. Isa Musa Kumurya – Mai ba da Shawara, Marshals
7. Hajia Fatima Abubakar Amneef – Mai ba da Shawara a fannin wayar da kan Jama’a
8. Comrade Nura Iro Ma’aji – Mai ba da Shawara kan ɗaukar Ma’aikata.