Kasar Sin ta ci gaba da amfani da kaso mai yawa na wutar lantarkin da ake samarwa daga makamashin iska da hasken rana, kamar yadda wasu bayanai da mahukunta suka fitar a ranar Lahadi suka nuna, inda hakan ya tabbatar da kokarin da ake yi na amfani da sabon makamashi a kasar, ya samu karin tagomashi cikin hanzari da kuma inganci, a fafutukar kyautata muhalli.
Kason amfani da lantarkin makamashin iskar da hasken rana, ya ci gaba da kasancewa da fiye da kashi 95 cikin dari a wannan shekarar, bisa bayanan da hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta fitar. Ana sa ran zuwa karshen shekarar nan ta 2024, lantarkin da ake janyowa daga iska za ta kai karfin kilowatts miliyan 510, yayin da na bangaren makamashin hasken rana kuma zai kai kilowatts miliyan 840.
- Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Muhimmiyar Makalar Xi Mai Taken “Zurfafa Aiwatar Da Juyin Juya Halin Jam’iyyar Kwaminis Ta Sin”
- Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Ya Kaddamar Da Cibiyar Raya Al’adu Da Kasar Sin Ta Ba Da Tallafin Ginawa
A cikin watanni bakwai daga farkon wannan shekarar, an janyo lantarki ta makamashin iska da hasken rana na jimillar sa’o’in kilowatts tiriliyan 1.05, inda hakan ya kai kimanin kashi 20 cikin dari na adadin lantarkin da kasar Sin ta janyo.
Masana’antar sabon makamashi ta kasar Sin dai ta ci gaba da samun habaka a ‘yan shekarun nan, yayin da take ci gaba da samun bunkasa da kaso fiye da goma a ko wace shekara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)