Kwanan nan Majalisar Dinkin Duniya, da gwamntocin kasashe daban-daban, sun ci gaba da mayar da martaninsu, inda suka yi Allah wadai da ziyarar kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi a yankin Taiwan, suna masu nuna adawa ga Amurka, saboda goyon-bayanta ga masu yunkurin balle Taiwan daga kasar Sin, tare kuma da jaddada matsayinsu, na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
Babbar darektar ofishin MDD dake birnin Vienna, Ghada Fathi Waly, ta sake nanata cewa, ofishinta yana girmama kudurorin babban taron MDD, da tsayawa tsayin daka kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
A nasa bangaren, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya yi jawabin cewa, kasarsa tana tsayawa haikan, kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma a ganinsa, hakan zai taimaka ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.
Shi ma firaministan janhuriyar Afirka ta Tsakiya, Felix Moloua, da ministar harkokin wajen kasar Sylvie Baipo Temon, duk sun jaddada goyon bayan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kira ga bangarori masu ruwa da tsaki, su mutunta alkawuran siyasa da aka yi tsakanin Sin da Amurka.
Sa’anan kuma, mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya bayyana cewa, kasar tana marawa kasar Sin baya, saboda kokarin da take yi, na kiyaye mulkin kai, da cikakken yankunan kasa, tare kuma da bukatar wasu kasashe da su dakatar da yunkurinsu na lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Ministan kula da harkokin gida na kasar Laberiya Nathaniel McGill, ya bayyana cewa, kasarsa ta riga ta ayyana doka kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana kasar ba ta yarda da duk wani yunkuri na sabawa hakan ba.
Shi kuwa Okello Oryem, karamin ministan kula da harkokin waje na kasar Uganda, cewa ya yi kasarsa, za ta ci gaba da tsayawa haikan, kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.
A cewarsa, ya dace kasashen yammacin duniya, ciki har da Amurka, su dakatar da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kana, Uganda tana goyon-bayan matakan da kasar Sin take dauka, domin tabbatar da mulkin kai, da kiyaye cikakken yankin kasar. (Murtala Zhang)