Jam’iyyar APC ta kara samun tagomashi a daidai lokacin da ‘yan majalisan adawa na jam’iyyun PDP da LP suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Jam’iyya mai mulki na ta kara karfi, yayin da jam’iyyun adawa ke kara samun rikicin cikin gida gabanin zaben 2027.
- Yadda Sin Da Kasashen Afirka Ke Hadin Gwiwar Zamanantar Da Ayyukan Noma
- Mun Karbi Rancen Dala Biliyan 1 Don Tallafa Wa Matatar Man Dangote —NNPC
A yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, ana kara rage kima da martabar jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar LP da kuma PDP.
Yayin da jam’iyyar PDP ke fama da rigingimun cikin gida wanda ya kai ga ficewar wasu ‘ya’yan jam’iyyar, a halin yanzu jam’iyyar LP ce ta fi fama da rikicin cikin gida, inda ta aka fi samun sauyin sheka a tsakanin ‘ya’yanta.
A cewar manazarta, sauya shekar da ke ci gaba da gudana tun bayan fara zaman majalisar dokokin kasar nan karo na 10 a shekarar 2023, tuni aka fara samun gagarumin tasiri a siyasance, musamman ga irin tasirin da jam’iyyar ke da shi da kuma tsayuwar daka a majalisun tarayya guda biyu.
Tun bayan kaddamar da majalisa ta 10, jam’iyyar LP tana da ‘yan majalisa ‘yan tsiraru a zauren majalisan kasar nan.
Kamar yadda sakamakon zaben 2023 ya nuna, jam’iyyar ta samu kujeru 35 a majalisar wakilai, wanda hakan ya samu karin girma daga zabukan da suka gabata, saboda farin jinin dan takararta na shugaban kasa, Mista Peter Obi, da kuma yadda jam’iyyar ta mayar da hankali kan matasa da kawo sauyi.
Wannan adadin kujeru na wakiltar ya kara wa jam’iyyar kima, inda ya sanya ta a matsayin wata jigo a majalisar.
Sai dai jam’iyyar LP ta sha ganin ficewar mambobinta zuwa wasu jam’iyyun siyasa, musamman jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
‘Yan majalisar da suka jefar da LP sun hada da Tochukwu Okere (Imo), Donatus Mathew (Kaduna), Bassey Akiba (Kuros Ribas), Iyawe Esosa (Edo) da Daulyop Fom (Filato).
Wannan yunkurin ya rage karfin lambobin LP a cikin zauren majalisa.
A ranar 12 ga watan Disamba, 2024, adadin mambobin jam’iyyar a majalisar wakiali ya ragu daga 35 zuwa 17, wanda hakan ke nufin jam’iyyar ta yi asarar kujeru 18 a cikin shekara daya da rabi.
A majalisar dattawa kuwa, Sanata Francis Onyewuchi, wanda ya wakilci Imo ta Gabas a karkashin jam’iyyar LP, shi ma ya fice daga jam’iyyar zuwa APC.
Rikicin cikin gida da ke tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar LP a matakin kasa da kuma zargin kutsawa da wakilan jam’iyyar APC mai mulki ke yi babu shakka ya taka rawa a cikin abubuwan da ke na sauya sheka.
Ita kuwa jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa Hon. Erhiatake Ibori-Suenu, mamba mai wakiltar mazabar Ethiope ta Jihar Delta, inda ta sauya sheka zuwa APC.
Ga dukkan alamu an fara cin PDP da yaki. Mambobin kwamitin gudanarwa wadanda ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na jam’iyyar, har yanzu ba su gama farfadowa ba daga yakin da ake yi na kaka-nika-yi da ya yi sanadin tarwatsa jam’iyyar.
Sakamakon haka, yayin da shugabannin jam’iyyar masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ke murnar kiran da kwamitin amintattu (BoT) ya yi na a samar da wanda zai maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, wadanda muradinsu ya yi daidai da na ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na shirin ci gaba da rike mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Amb. Umar Damagum, a ofis.
Wike, wanda shi ne shugaban gwamnonin G-5, kungiyar gwamnonin PDP da suka taka rawa a yunkurin jam’iyyar na neman mulki da Bola Tinubu a 2023, sun ci gaba da zama a cikin jam’iyyar kuma da alama za su yi wa Tinubu aiki a karo na biyu a 2027.
An tabbatar da cewa ajiye Damagum a ofis har zuwa Disamba 2025 lokacin da wa’adin Ayu ya kare a hukumance zai biya bukatun bangaren su Wike.
Domin cimma manufofinsa, ya zuwa yanzu wannan bangaren Wike ya yi nasarar sauya taron kwamitin zartaswa na kasa na jam’iyyar zuwa wani matsayi sau uku a jere tun daga watan Maris din 2024, wanda hakan ya tsawaita zamansa.
Ana sa ran za a yanke shawara kan ko za a zabi sabon shugaban jam’iyyar ko kuma Damagum za a bar shi ya ci gaba da aiki a taron na kwamitin zartarwa na jam’iyyar.