A ranar Laraba ce, Shugaban kasa Bola Tinubu ya gurfana a zauren hadakar majalisun tarayya guda biyu domin gabatar da kudirin kasafin kudin 2025 na naira triliyan 47.9.
Akwai muhimman bangarori da suka fi samun kaso mai tsoka a cikin kasafin kudin na 2025. Inda bangaren tsaro ya yi zarra da naira triliyan 4.91.
- Yahaya Bello Ya Samu Beli Bayan Cika Sharudan Kotu
- Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kara Wa Hukumar NEPC Kudaden Aiki
Sannan bangarorin kayayyakin more rayuwa, Lafiya, da Ilimi za suka samu naira tiriliyan 4.06, naira tiriliyan 2.48 da kuma naira tiriliyan 3.5, bi da bi.
Kudirin kasafin kudin mai taken, “Kudirin kasafin kudi na maidowa da tabbatar da zaman lafiya da samun nasara.”
Tinubu ya bayyana cewa, “Babban abin da ke cikin kasafin kudin 2025, bangaren tsaro ya samu naira tiriliyan 4.91, bangaren samar da ababen more rayuwa ya samu naira tiriliyan 4.06, bangaren lafiya ya samu naira tiriliyan 2.48, sannan kuma bangaren ilimi ya samu naira tiriliyan 3.5.
“Yayin da muka fara aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025, za mu dauki matakan na ba sani, ba sabo, mun yanke shawarar musu muhimmanci, kuma abubuwan da muka sa a gaba a bayyane suke. Wannan kasafin kudin yana nuna sabon alkawari na karfafa tushen tattalin arziki mai karfi.
“A duk lokacin da muke gyara muhimman sassa masu mahimmanci domin samun ci gaba, muna sa ran tabbatar da tsaron kasarmu. Tsaro shi ne ginshikin duk wani ci gaba. Mun kara wa sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro kudade sosai don tabbatar da tsaron kasa da kare iyakokinmu da kuma karfafa ikon gwamnati a kan kowane farfajiyar kasarmu.”
Tinubu ya tabbatar da cewa, “Gwamnati za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro kayayyakin aiki na zamani da na’urorin zamani da suke bukata domin kare lafiyar al’umma, da inganta tarbiyyar maza da mata a cikin rundunar soji shi ne babban abin da gwamnatinmu ta sa a gaba, manyan jami’an tsaro maza da mata na sojojinmu da na ‘yansandan Nijeriya za su kare al’ummarmu, gwamnatinmu za ta ci gaba da ba su karfin gwiwa domin murkushe ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da kuma masu barazana ga ’yancin kanmu.”
Da yake jawabi kan kasafin kudin, Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa za a tsawaita tsawon lokacin kasafin kudin shekarar 2024 zuwa ranar 25 ga watan Yunin 2025.
Ya bayyana haka ne cikin jawabinsa na bude taron gabatar da kasafin 2025 da Shugaba Tinubu ya yi a zauren hadakar majalisun tarayya wanda ya kunshi majalisar dattawa da ta wakilai.
A cewarsa, kaso 50 ne na kasafin kudin shekarar 2024 ya aiwatu, inda ya bar gibin kaso 50 da ba a aiwatar ba, don haka, akwai bukatar tsawaita lokaci don aiwatar da shi yadda ya dace.