Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ta yi kira da Shugabannin majalisun dattawa da wakilai da cewar su dauki matakan da suka kamata wajen kare hukumar gidauniyar manyan makarantu (TETFund) daga cikin tsarin dokar samar da gyara a al’amuran haraji na shekarar 2024.
A wani jawabin data fitar ranar Jumma’a ta makon daya gabata wadda ke dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na kasa,Farfesa Emmanuel Osodeke, ta yi kakkausar sukar cewar dokar idan aka amince da ita a yadda take, zata samar da cikas kan irin muhimmin taimakon da hukumar take badawa ta bangaren ci gaban ilimi.
- Kudin Kirifto: An Cafke Dan Nijeriya Da Laifin Damfarar ‘Yan Australiya Dala Miliyan 8
- Bangarorin Da Suka Fi Samun Kaso Mai Tsoka A Kasafin Kudin 2025
“Kungiyar ASUU tana sane da duk halin da ake ciki na maganganun da ake dangane da kawo gyara da samar da doka a tsarin haraji a Nijeriya a shekarar, 2024,wanda a yanzu lamarin yana gaban majalisun kasa.Daga cikin dokar haraji akwai maganar za ayi gyara a dokar harajin daya shafi ilimi kamar yadda lamarin yake,”.
Abin da akwai daure kai da ban takaici, domin kuwa sashi na 59 karamin sashi na(3)na dokar ya bayyana cewa kashi 50 na harajin ci gaba za a ba TETFund a shekarun 2025 da 2026 yayin da hukumomin NITDA,NASENL da NELFUND za su raba sauran kashi 50 da ya rage.
Kamar dai yadda lamarin ya ke cewar kungiyar ta ASUU, TETFund, za ta samu kashi “66.7 a shekarar 2027, 2028 da kuma 2029 na shekarun da ake gwada shi lamarin daga nan kuma gaba babu wani abu.
“ASUU ta damu kwarai dangane da wannan lamari mai hadari na sabuwar dokar haraji,da ake kira harajin ci gaba inda duk wasu tsare- tsaren TETFund za a maida su ga sabuwar hukuma mai suna gidauniyar bada bashin ilimi ta kasa (NELFUND).
“Gaskiyar lamarin shi ne a sanadiyar sabuwar dokar haraji idan har aka amince da ita abin yana nufin daga shekarar 2030, dukkan kudaden da aka samu da suna gidauniyar ci gaba za a rika tura sune zuwa hukumar NELFUND. ASUU tace shi abin ba ma kawai yana da ban takaici bane domin kuwa idan aka kalli ci gaban kasa akwai babbar matsalar da ita hukumar TETFund za ta shiga.
“ASUU ta ci gaba da bayani inda ta ce ba zata kame hannuwanta ba tana ganin ana kokarin kawo karshen ita hukumar TETfund, wadda ita ta kasance ne a matsayin abinda ya biyo bayan zaman da aka yi tsakanin ita kungiyar da gwamnatoci suka yi tun shekarar 1992. A namu ganin idan aka yi gyara a dokar da aka yi a shekarar 2011 ta TETFund, ko dai kawai don ana son ayi hakan ne saboda wani dalili, ba karamin ci baya bane ga lamarin daya shafi ilimi bane kadai, har ma Nijeriya a matsayin ta na kasa.
“Wannan shi yasa domin haka ne, ASUU tana kira majalisun kasa musamman ma Shubannnin majalisun dattawa da ta wakilai ta tarayya, su yi duk iyakar iyarsu su kare TETFund kada ayi amfani da dokar kawo gyara haraji ta 2024,har a kai ga samun damar tarwatsa ta kamar yadda sanarwar ta bayyana.