“Ku tashi mu farka ‘yan Arewa Ku san bacci aikin kawai ne” in ji Marigayi Dakta Alhaji Mamman Shata Katsina.
Wannan shi ne baitin wakar da marigayi Alhaji Dakta Mamman Shatan Waka, Shata Katsina mawakin Arewa ya yi domin tunasar da mu abin da ya kamata mu yi a matsayin mu na ‘yan Nijeriya ya kamata mu sani, to yanzu an wayi gari Arewa na cikin yanayin dimuwa da tashin hankali a kan yadda Nijeriyarmu ke tafiya a matakin rashin tsaro da rashin sanin makomar kasar a kakar zaben 2023 da ke fuskantowa, talaka da masu hannu da shuni da mahukuntan kasar ba mu da wata kasa da muke alfahari da ita tamkar wannan kasar.
- Sabon Fim din JAMILA Zai Fara Haskawa A Makon Nan –Hafsat Sa’eed
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Shin me ya sa talaka zai zuba ido a kan wani abin da bai taka kara ya karya ba ko kuma a ce wasu ‘yan canjin Nairori da za a bashi a yayin zabe ya kuma bayar da kasar tamu ta gado ga hannun ‘yan jari hujja wadanda su ba kasar ce a gabansu ba.
Idan ba a manta ba, a lokacin da jam’iyyar APC ke babban gangaminta na farko a Abuja a kafin zaben shekarar 2015, Audu Ogbe ya hau Mimbari ya shelanta wa talaka cewa ‘BringBackOurGirl,’ kungiyarsu ce, kuma suna goyon bayan abubuwan da take.
Yau kuma an wayi gari ita dai jam’iyyar ta APC ta ki amincewa da duk wata kungiya ko wasu gungun al’umma da za su fito domin su nuna ranshin goyon ko rashin jin dadin tsarin mulkin da take gudanarwa a Nijeriya.
A shekarar 2006 da 2007, lokacin da Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ke kokarin yakin neman zabensa karo na biyu na wa’adin mulkinsa, an samu wani gagarumin tashin hankalin da ya faru a wannan tsakanin na kisan babban Shehin Malami Sheikh Malam Ja’afar Mahmud Adam, wanda wannan ne sanadiyyar bullar wata kungiya mai suna Taliban a wancan lokacin a Jihar Kano dake da’awar cewa ana kashe manyan Malamai a kasar kuma hukuma ba ta daukar mataki a kan hakan ba.
Wannan ya sa suka zo domin fada da jami’an tsaro, al’ummar gari suka goyi da bayansu, aka kuma basu hadin kai wanda wannan ya sa suka ci karensu ba babbaka a kan jami’an tsaro, inda suka kai farmaki a wuraren kamar irinsu ofisoshin ‘yan sandan Sharada da na Fanshekara, inda suka yada zango, kuma suka yi sansani a nan unguwar ta Fanshekara, hakan ya jawo har mazauna unguwar ta Fanshekara yin gudun hijira zuwa cikin gari, bayan wani lokacin da bai wuce kwana uku zuwa hudu ba, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya fito ya shelanta cewa su dai sun yi nasarar korarsu daga jihar, amma babu takamaiman yadda aka yi suka bar jihar, dama ba mutanen Kano ba ne, zuwa suka yi jihadi a cewarsu.
Daga bayan nan mutanen Nijeriya suke zargin cewa kamar wannan kungiya da ta yi da’awar jihadi a wancan lokacin ita ce ta shirya kuma ta gudanar da kisan Malam Ja’afar. Haka kuma ita wannan kungiya ita ce ta rikidide zuwa kungiyar Boko Haram da take ayyukan ta’addancinta a tsakanin Arewa maso Gabashin Nijeriya, gefen Chadi, gefen Kamaru da kuma gefen kasar Nijar.
Tarihi kuma bai manta da ita wannan kungiya na da’awar cewa karatun Boko Haramun ne, amma kuma da suka fara fada da hukumomin tsaron gwamnati daga baya kuma sai suka koma kan mai uwa da wabi, kan duk wani dan Nijeriyar da baya goya musu baya, kuma har yanzu sun kasa ba da hujjar da ta sa suke takama da ita na cewa ilimin Boko haramun ne.
Yan’ Nijeriya, mu kula, mu gane cewa duk wata takama da muke yi, muna yin ta ne sakamakon zaman lafiya da kuma gagarumar gudunmawar da jami’an tsaron kasar Nijeriya ke bamu, amma idan kuma muka zuba ido ‘yan ta’adda suka ci gaba da keta wa jami’an tsaron Nijeriya haddi to wallahi wannan kwanciyar hankalin da zaman lafiyar da muke takama da su sai ta zame mana kunci da bakin ciki, don da an gama da su kan ‘yan Nijeria da basu san hawa da sauka ba za a dawo, mu talakawan Nijeriyar da bamu da wata kasar da tafi Nijeriya.
Menene dalilin da ya sa talaka ke goyon bayan cin mutumcin jami’an tsaron Nijeriya, shin shi jami’in tsaro wani mutum ne daban ba iri daya da mutane ba, ko shi ba daga cikin mu ya fito ba, idan kuma daga cikin mu ya fito me ya sa muke goya wa ‘yan ta’adda baya su ci mutunci jami’ansu, kada talaka ya manta shi fa jami’in tsaro, da ne kamar dan kowa, kuma uba ne kamar yadda uban kowa yake, kuma yayan wasu ne kuma kanin wasu ne.
Abin da talaka kullum yake manta wa shi ne, shi fa jami’in tsaro mutum ne wanda ya sadaukar da jin dadinsa da jininsa don talaka ya kwanta cikin aminci ya tashi cikin aminci da kwanciyar hankali, jami’in tsaro ne da ya sadaukar da jininsa da lokacinsa domin tsaron dukiyoyi da rayukan ‘yan kasa, mu talakawa mu yi hobbasa domin taimaka wa jami’an tsaron kasar nan, tun daga matakin dansanda, soja da dukkan wani dogari mai damara da mara damara duk suna bukatar gudunmuwarmu talakawan Nijeriya domin su gudanar da aikin su kamar yadda ya kamata.
Ita kuma gwamnati ita ce da babbar gudunmuwar bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya. Hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin Nijeriya ta tabbata ta sauke dukkan nauyin jami’an tsaron da ya rataya a wuyan ta, babu yadda za a yi ka dauki mutum aiki kuma ka bashi makami kuma ka barshi da yunwa, har yanzu ina neman sanin shin kasafin kudin da ake gabatarwa majalisar kasa kowacce shekara shin ko sun taba bin diddigin kasafin kudin jami’an tsaron Nijeriya sun ga tabbacin abubuwan da aka saka cikin an tanadar musu kudin ko kuma kayan aikin da aka ce za a tanadar musu a cikin kasafin ya tabbata?.
Me ya sa ba a tanadar wa jami’an tsaro kayan aikin na zamani ba, gwamnati ki taimaka ki kula da kasafin kudin jami’an tsaro da lafiyarsu, da matsuguni, da magunguna a asibitocinsu, domin zaman lafiya da kwanciyar hankalinsu shi ne kula da tsaron kasarmu.
Ku tuna fa ‘yan Nijeriya Jami’an tsaro su ne, suka zaunar da Nijeriya a matsayin gamayya Nijeriya, ba don jajircewarsu ba da tuni wani labarin ake ba wannan ba, ko lokacin da Ojukwu ya yi tawaye jami’an tsaro ne suka hana shi tabbatar da kudurinsa na fasa Nijeriya gida biyu domin kafa kasar Biafara, talaka ya kalli tarihi ko don taimaka wa jami’an tsaro. Tarihi na da muhimmanci.