Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon jaje ga shugaban kasar Mozambique Filipe Jacinto Nyusi, sakamakon mahaukaciyar guguwar Chido da ta aukawa kasar.
Cikin sakon da ya aike a jiya, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya samu labarin cewa, mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun jikkata, kuma an samu hasara da dama sakamakon ibtila’in. Ya ce a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, yana jajantawa mutane da iyalan wadanda ibtila’in ya rutsa da su. Ya ce, a wannan lokaci, jama’ar kasar Sin da jama’ar Mozambique suna tare da juna, kuma Sin tana son bayar da gudummawa ga Mozambique wajen sake gina kasar bayan ibtila’in. (Zainab Zhang)