A wata sanarwa da Kakakin Rundunar Tsaron Farar Hula (NSCDC) ta Jihar Kano, SC Ibrahim Idris Falala, ya fitar, ya bayyana cewa rundunar ta shirya tsaf don tabbatar da tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara ta 2025.
Ya ce rundunar za ta jibge jami’anta 3,542 a muhimman wurare daban-daban a fadin Jihar Kano domin kare lafiyar al’umma da tabbatar da bin doka da oda a lokacin bukukuwan.
- An Bude Sabon Babi A Yankin Macao Wajen Aiwatar Da Manufar Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu A Cikin Shekaru 25
- Tsarin Tinubu Kan Raya Albarkatun Kiwo Da Samar Da Abinci Yana Haifar Da Ɗa Mai Ido – Minista
Wannan matakin, a cewarsa, na da nufin tabbatar da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
Haka kuma, SC Ibrahim ya tabbatar da cewa jami’an NSCDC za su yi aiki ba dare ba rana a kananan hukumomi 44 na jihar, tare da neman goyon bayan al’umma da addu’o’insu don samun zaman lafiya da ci gaban Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.