ALHAJI DAHIRU BUBA MADAGALI, shi ne shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta kasa (IKMAN), reshen jihohin Adamawa da Taraba.
Wakilinmu na Jihar Adamawa, MUHAMMAD SHAFI’U SALE ya tattauna da shi kafin karin kudin mai da canja tsarin NNPC, kan matsalolin da suka dabaibaye harkokin man fetur, karancinsa, karkatar da shi, da wahalhalun da jama’a ke sha.
- Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas
- Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan
Ga yadda hirar ta kasance kamar haka:
Masu karatunmu za su so ka gabatar musu da kanka.
Sunana Alhaji Dahiru Buba, haifaffen Madagali. Ina zaune a Yola kusan shekarau 30, ina gudanar da harkokin kasuwancina har Allah ya kai ni wannan lokacin da aka zabe ni shugaban IKMAN a jihohin Adamawa da Taraba.
Ina shugabancin jihohi da yawa ne, saboda bisa dokar man fetur ana bin deport ne ba jiha ba, kamar Adamawa an hada ta da Taraba, yayin da Gombe aka hada ta da Bauchi, Borno an hadata da Yobe, to haka ne ayyukanmu na kasuwancin gashinkai ke bin tsarin dokar Nijriya.
Ka yi maganar cin gashinkai, wani karin haske za ka yi game da gashinkan da kake nufi?
A dokance, kafin ka gina gidan mai, sai ka tuntunbi gwamnati, sannan za ka kira jami’an ‘yan sanda su tabbatar da filin wurin yana da kyau, haka kuma za ka kira jami’an kashe gobara su je su duba wurin ta yadda ba za a samu gobarar da za ta addabi jama’a ba, za ka tafi hukumar tsara birane da kuma ma’aikatan muhalli duk su saka maka hannu da sauran su.
Daga nan kuma za ka soma zuwa sashin hukumar kula da man fetur (DPR) domin amince maka ka gina gidan mai.
Idan ka kammala gina gidan mai, hukumar DPR za su baka lassis (takardan amincewa), sai ka rumgumi lassis da sauran takardunka ka tafi NNPC, ka je ka shiga yarjejeniya tsakaninka da gwamnati da shugaban kamfanin mai na kasa (NNPC) da sakataren NNPC, za ku sa hannu a kan yadda za a baka mai.
Idan kana da tanki guda hudu wanda ya kai 45, shi ne za a ci gaba da baka kowace rana, kai za ka yi yadda za ka sayar da shi, sannan kuma a sake baka wani.
Sai dai kuma a yanzu gwamnati ta rushe wannan yarjejeniya, inda a yanzu haka ba mu san alkiblarmu ba. A baya, za ka shugaban deport ke sayar da man a madadin NNPC, amma a yanzu gaba daya komi ya koma Abuja hannun shugaban NNPC.
Idan kana da gidan mai guda daya kuma banki yake taimaka maka da kudaden kawo man, sannan kuma an ce yau a Nijeriya mutum daya ne zai sa maka hannu kafin ka samu mai dole a samu matsala.
Wannan shi ne dalillin da ba ma samun mai, wanda ta kai muna sayan man daga hannun wasu da ake takaita sunansu da MOMAN, kuma suna sayar manada mai da tsada.
A baya ana sayar mana da man kan Naira 166, amma yanzu an kara ana sayarwa a boye wanda kudin mai ya koma 185.
A takaice dai a halin da muke ciki yanzu, maganar mai babu wanda zai gaya maka tabbacin ga halin da ake ciki, domin maganar mai ta zama ba ta da alkibla gaba daya.
Wato rashin aiki da yarjejeniyar da ke tsakaninku da gwamnatin tarayya ya haifar da karancin mai, wanda hakan ya jefa ‘yan Nijeriya halin da suka samu kansu a yanzu na karancin mai.
NNPC yana cewa yana raba mai kamar yadda ya saba, ku kuma kuna cewa ba a ba ku man, ina man ke shiga?
Wasu ‘yan kalilan mutane ne ake ba su, idan an ce maka ana ba da mai, ana bai wa A.A Rano da Shafa da Mai Kifi da dan Marna da Shema kadai, to wadannan kalilan mutane idan sun yi yawa su kai mutum 10, su ake bai wa man a Nijeriya gaba daya. Kuma a jihohin Adamawa da Taraba kwai muna da dillalan mai da suka kai dubu guda, balle a ce gaba daya Nijeriya.
Idan ka yi lissafi a Nijeriya muna da dillalan man fetur da suka haura dubu 30 da gudanar da harkokin mai. Amma a cikin bai wuce mutum 10 ake ba su mai ba, sannan a zo a ce ana ba mu mai, mu ba a ba mu mai ba, idan an ba mu kuma a fid da sunayenmu da yawan man da aka ba mu.
Wannan yanayin da ‘yan Nijeriya ke ciki a yanzu, ka ce an yi karin kudin mai a boye, ta yaya za ku fuskanci ‘yan Nijeriya?
To, ni kam na san yanda muka fuskanci wahala ne zai karu a kan wahala, yanzu ma muna sayen shinkafa dubu 35 a kan buhu guda, ko da yake NNPC sun ce za su ci gashin kansu ta yadda za su kawo kaya su sayar wa wadanda suke bukata.
Ina tabbatar wa gwamnati da ‘yan Nijeriya cewa, idan gwamnati ta ga cewa man nan ba za ta iya kawowa ba, ta tsamu hannunta ta mayar mana da shi tare da sayar mana da dala a farashi mai rahusa duk inda mai yake za mu iya kawowa har ya wadaci talakawan Nijeriya.
Wato dai kana jin ku za ku iya wadatar da ‘yan Nijeriya da mai tun da gwamnati ta gaza?
Wallahi za mu iya wadatarwa idan gwamnati ta ba mu izini, ta ba mu lasisi kamar yadda ta ba mu muka gina gidan mai. Idan gwamnati ta zabi wadanda za su iya ta ba su lasisi, wallahi za mu kawo mai da zai wadatar da Nijeriya, kuma shi zai kawo karshen matsalar man in Allah ya yarda.
Wani tabbaci kake da shi cewa idan kuka samu laisisin ba za a samu wata matsala ko karancin man ba?
Shi dan kasuwa a ko da yaushe dan kasuwa ne, wannan kuma shi ne kasuwancinmu, a cikinmu akwai mai gidajen mai 10, akwai mai gidan mai 20 a kwai mai 5, akwai mai gidan mai 1, gidan mai kuma idan ka gina ba ka sayar da mai ya zama kan go, to mene ne zai hana mu sayo wadataccen man. Wannan shi ne mafita a kan matsalolin man da muka tsinci kanmu a ciki.
Me kuke son ‘yan Nijeriya su fahimta game da ayyukanku?
Yauwa, al’ummar Nijeriya ina son su fahimci cewa matsalar mai ba daga wajanmu ba ne, yana hannun NNPC ne.
Matsalar rashin biya a shannun PEUM yake, DPR ba su da damuwa da mu. Mutum daya yake shugabantar hukumomin DPR, PPR da PEUM, amma ina tabbatar maka daga lokacin aka hada su a wuri daya zuwa yau ba mu gane mene muke a harkar man ba, domin babu wanda zai ce maka yau an biya shi kudinsa ban da mutanen da na kirga makannan.
Wannan kasuwancin na bukatar a sake dubawa, idan har gwamnati za ta biya mu hakkinmu, to komin zai daidaita, kuma in sha Allahu idan an yi haka kowa zai gani a kasa.