• English
  • Business News
Thursday, August 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Da Darakta Janar Na VON Sun Yi Alhinin Rasuwar Babbar ‘Yar Jarida, Rafat Salami

by Sulaiman
8 months ago
in Labarai
0
Minista Da Darakta Janar Na VON Sun Yi Alhinin Rasuwar Babbar ‘Yar Jarida, Rafat Salami
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalan Hajiya Rafat Salami, babbar ‘yar jarida a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) kuma Ma’ajin Cibiyar Yaɗa Labarai ta Duniya (IPI), wadda ta rasu a ranar Juma’a a Abuja.

Da yake bayyana rasuwar tata a matsayin “babban rashi ba kawai ga iyalan ta ba, har ma ga harkar aikin jarida ta Nijeriya,” ministan ya yaba wa sadaukarwar ta ga aikin jarida.

  • Babban Aikin “Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana A Wajen Da Ake Kiwon Kifi” A Sin Ya Fara Aiki
  • Kudirin Dokar Haramta Amfani Da Kudaden Waje Ya Tsallake Karatu Na Farko A Majalisa

Ya jaddada cewa ta shafe shekaru 23 tana aiki a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), inda ta kai matsayin Daraktar Sashen Watsa Labarai na Zamani, tana horar da matasa masu zuwa cikin masana’antar.

Labarai Masu Nasaba

’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato

NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya

A cikin saƙon ta’aziyyar sa, Idris ya ce, “Rasuwar ta ta bar babban giɓi a cikin ma’aikatan VON da kuma a IPI reshen Nijeriya, inda ta sadaukar da kan ta wajen kare haƙƙin ‘yan jarida, inganta ‘yancin yaɗa labarai, da tabbatar da jin daɗin ‘yan jarida, kuma kwanan nan aka sake zaɓen ta a matsayin ma’aji.”

Ya ƙara da cewa, “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalan ta da ma’aikatan VON, da IPI Nijeriya, da dukkan masana’antar aikin jarida a Nijeriya bisa rashin irin wannan fitacciyar mace. Allah ya jiƙan ta da rahama kuma ya bai wa iyalan ta ƙarfin jure wannan rashi.”

A nasa saƙon ta’aziyyar, Darakta Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace, ya bayyana Salami a matsayin “abar misali na ƙarfi, tausayi, da ƙwazo.”

Ya ce rasuwar ta ta bar dukkan iyalan VON cikin tsananin baƙin ciki.

Ya ce: “Misis Salami ba kawai ƙwararriya ba ce; ta kasance misali na ƙwarewa, gaskiya, da sadaukarwa.”

Ndace ya ƙara da cewa, “Gudunmawar ta ta ban-mamaki ga aikin jarida da rawar da ta taka wajen cigaban kafofin sadarwa na zamani a VON sun kasance abin a yaba.

“An san ta da aiki tuƙuru, iya yare da dama, da kuma jajircewa ga nagarta, ta kasance misali na ƙwarewa da ƙwazo.

“Dangantaka ta da Hajiya Salami ta fara ne kafin in zama Darakta Janar na VON. Bayan naɗin da aka yi mini, ko yaushe nakan nemi shawarwarin ta masu matuƙar muhimmanci kuma nakan dogara da goyon bayan ta wajen ƙoƙarin mu na gyara hukumar.”

Ndace ya bayyana cewa duk da matsalolin lafiyar ta, Salami ta taka rawar gani a wani taron da VON ta gudanar a baya-bayan nan.

Ya ce: “Na kira ta a lokacin taron don yi mata addu’ar samun lafiya, ban taɓa tsammanin wannan zai kasance maganar mu ta ƙarshe ba.”

Da yake tuna aikin ta a VON, Ndace ya bayyana rawar da ta taka wajen shirya shirye-shirye irin su VONSCOPE, Sixty to Minutes, da Africa Hour.

Ya ƙara da cewa: “Baya ga nasarorin ta na aiki, Hajiya Salami ta kasance mai ƙwarin gwiwa wajen al’amuran ƙungiyoyi, mai tsayin daka wajen kare daidaiton jinsi, kuma malama ga ɗimbin mutane a cikin masana’antar watsa labarai.”

“Shigar ta cikin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Ƙasa (NAWOJ), Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), da kuma sake zaɓen ta kwanan nan a matsayin Ma’ajin ƙungiyar IPI sun nuna jajircewar ta ta tsawon rayuwa wajen cigaban aikin jarida da kare haƙƙin ɗan’adam.

“Ta kasance Musulma mai tsantsar addini kuma memba mai aiki tuƙuru a ƙungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society, inda Salami ta zama abin misali na rayuwa cike da imani da hidima.

“Taimakon ta wajen ƙarfafa bayar da jini da kuma sadaukarwar ta marar yankewa wajen tallafa wa marasa lafiya sun zama alama ta jinƙai da tausayi nata.

“Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da ɗan ta, Ahmad, wanda take matuƙar ƙauna.

“Muna roƙon Allah (SWT) ya ba iyalan ta ƙarfin jure wannan babban rashi, kuma ya sa Aljannatul Firdaus ce makomar ta.”

“Tarihin Mqdam Salami na tausayi, juriya, da hidima za su ci gaba da kasancewa abin koyi gare mu har abada.

“Allah ya sanya kyawawan tunanin rayuwar ta ta ban mamaki da tasirin da ta bari su kasance masu kwantar da zuciya ga duk waɗanda ke jimamin rashin ta.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Babban Aikin “Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana A Wajen Da Ake Kiwon Kifi” A Sin Ya Fara Aiki

Next Post

Kirsimeti: Ugochinyere Ya Yaba wa Kyari, Dangote, da NMDPRA Kan Wadatuwar Man Fetur

Related

’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
Labarai

’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato

27 minutes ago
NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya
Manyan Labarai

NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya

1 hour ago
Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16
Labarai

Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16

4 hours ago
Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
Manyan Labarai

Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina

5 hours ago
Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara
Labarai

Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara

14 hours ago
APC
Labarai

2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara

15 hours ago
Next Post
Kirsimeti: Ugochinyere Ya Yaba wa Kyari, Dangote, da NMDPRA Kan Wadatuwar Man Fetur

Kirsimeti: Ugochinyere Ya Yaba wa Kyari, Dangote, da NMDPRA Kan Wadatuwar Man Fetur

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato

’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato

August 14, 2025
NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya

NAF Ta Kashe ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Wata 8 A Nijeriya

August 14, 2025
An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

August 14, 2025
Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16

Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16

August 14, 2025
Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina

Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina

August 14, 2025
Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara

Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara

August 13, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu

August 14, 2025
Gyaruwar Alakar Kasuwancin Sin Da Amurka Ta Zarce Bukatun Kasashen Biyu

Gyaruwar Alakar Kasuwancin Sin Da Amurka Ta Zarce Bukatun Kasashen Biyu

August 13, 2025
APC

2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara

August 13, 2025
Sin Ta Dauki Matakan Mayar Da Martani Kan Bankuna Biyu Na EU

Sin Ta Dauki Matakan Mayar Da Martani Kan Bankuna Biyu Na EU

August 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.