Gwamnatin tarayya ta sanar da ɗage haramcin haƙar ma’adanai da ta sanya na tsawon shekaru biyar a jihar Zamfara, da zummar magance taɓarɓarewar harkokin tsaro a yankin.
Ministan ma’adanai Dokta Dele Alake, ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce matakin ya biyo bayan ci gaban da aka samu a fannin tsaro da suka haɗa da kashe manyan ‘yan fashin daji da kuma kame ƙasurgumin kwamandansu Halilu Sububu.
- Kofin Duniya: FIFA Ta Fitar Da Yadda Za A Samu Gurbin Zuwa Amurka
- Wike Ya Bai Wa Asibitocin Gwamnati Umarnin Tallafa Wa Wadanda Turmutsitsin Abuja Ya Rutsa
Dokta Alake, ya yi ƙarin haske kan tarin zinari da sauran ma’adanai da ke Zamfara, inda ya jaddada cewa dawo da ayyukan haƙar ma’adinan zai farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma habaka kudaden shiga, wanda ya ce sanya dokar da farko ya zama dole saboda dalilan taɓarɓarewar tsaro.
Har ila yau, ya yi tsoƙaci game da wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ƙasar Faransa, wanda ya fayyace cewa ta shafi tallafin fasaha da kuɗi ne kawai don ɓunƙasa ma’adanan, ba wai yarjejeniyar soji ba ko sarrafa albarkatun ba.
Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin cewa ɗage dokar zai samar da ayyukan yi da kuma tallafawa ci gaban tattalin arziƙin ƙasa tare da kiyaye tsauraran matakan tsaro don kare yankin.