Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalai da ‘yan’uwan waɗanda suka rasa rayukan su sakamakon turmutsitsi yayin rabon abinci da aka yi a Ibadan, Okija da Abuja.
A cikin wata sanarwa da Rabi’u Ibrahim, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai ga Ministan, ya fitar a ranar Lahadi, ya ruwaito Idris yana cewa: “Tunanin mu da addu’o’in mu suna ga waɗanda suka rasa rayukan su da iyalan su da duk wanda wannan mummunan al’amari ya shafa.”
Ministan ya ce waɗannan abubuwan baƙin ciki sun yi matuƙar girgiza gwamnati kuma ya jaddada muhimmancin tabbatar da gudanar da taron jama’a yadda ya kamata yayin gudanar da irin waɗannan ayyukan alheri, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Duk da yake ya yaba da kyawawan niyyar waɗanda suka shirya irin waɗannan ayyuka domin taimaka wa mabuƙata, ministan ya gargaɗi dukkan mutane da ƙungiyoyi da suke shirin gudanar da irin waɗannan ayyukan da su bi umarnin da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mista Kayode Egbetokun, ya bayar kan a riƙa tuntuɓar ofisoshin ‘yan sanda domin gudanar da tsari mai kyau na kula da jama’a da tsaro.
Ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jami’an ‘yan sanda da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) yana da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka da tabbatar da cewa irin wannan ƙoƙarin na agajin mabuƙata bai haifar da wata damuwa ba.
Haka kuma Idris ya yi kira ga ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji siyasantar da irin waɗannan mummunan al’amuran, yana mai bayyana cewa waɗannan munanan al’amura ba su da alaƙa da tada komaɗar tattalin arziki na gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi.
“Ya kamata a lura da cewa a baya an taɓa samun aukuwar irin waɗannan abubuwan takaici, kafin zuwan wannan gwamnati mai ci, don haka duk wani yunƙuri na danganta waɗannan bala’o’i da gyare-gyaren Shugaban Ƙasa ba shi da tushe kuma ba gaskiya ba ne,” inji shi.
Idris ya ce gyare-gyaren da ake yi, yayin da suke sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya domin samun cigaba mai ɗorewa, an tsara su ne domin inganta rayuwar dukkan ‘yan Nijeriya, musamman mabuƙata, ba tare da haifar da wata damuwa ba.
Ministan ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su haɗa kai wajen tabbatar da cewa lokacin bukukuwan Kirsimeti ya kasance lokacin zaman lafiya, kyakkyawan hali, da farin ciki, ba tare da abubuwan baƙin ciki da za a iya kauce wa ba.