Tattaunawar kafafen yaɗa labarai ta farko da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu za ta gudana a daren yau Litinin, inda zai samu damar yin bayani kai tsaye ga ‘yan Nijeriya kan batutuwa daban-daban.
Wannan sanarwa ta fito ne a wata gajeriyar takarda da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin watsa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya hannu a kai yau Litinin da yamma.
- Dangote Ya Yabi Tinubu Kan Tasirin Yarjejeniyar Musanyar Fetur da Naira
- Tsarin Tinubu Kan Raya Albarkatun Kiwo Da Samar Da Abinci Yana Haifar Da Ɗa Mai Ido – Minista
Za a yi wannan tattaunawa kai tsaye da ƙarfe 9 na dare, ranar Litinin, 23 ga Disamba, kuma za a nuna shi a gidan talabijin na NTA da tashar rediyo ta FRCN. An kuma umarci tashoshin talabijin da na rediyo a faɗin ƙasa su haɗa kai don watsa hirar don isar da saƙon ga al’umma gaba ɗaya.
Tattaunawar, wacce ita ce ta farko a ƙarƙashin mulkin Tinubu, ana sa ran za ta bayyana manufofin gwamnatinsa, nasarori, da shirye-shiryen da yake da su nan gaba yayin da ƙasar ke fuskantar manyan ƙalubale.