Shugaba Bola Tinubu, ya kare adadin yawan mutanen da ke cikin gwamnatinsa, wanda ya ƙunshi ministoci 48 da kuma wasu Masu Ba da Shawara na Musamman, inda ya ce hakan ya zama dole domin samar da ayyuka masu tasiri a ƙasa.
A cikin hira ta farko da Shugaba Tinubu ya yi da manema labarai, wanda aka yi a daren ranar Litinin a gidansa da ke Legas, ya tabbatar da cewa, “Ba na rage yawan ministocina ba.”
- Ban Taɓa Nadamar Cire Tallafin Man Fetur Ba – Tinubu
- ACG James Sunday Ya Yi Bikin Cika Shekaru 35 A Aikin NIS
Ya bayyana cewa zaɓen ministocin yana da nasaba da inganci da buƙatun ƙasar.
Tinubu, ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai girma tare da mutane sama da miliyan 200, kuma shugabancin irin wannan yawan al’umma na buƙatar shugabanni da dama.
“Idan kana so ka kula da mutane sama da miliyan 200, kana buƙatar yawan yawan masu kula da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yawan ministoci da masu ba da shawara suna da muhimmanci wajen gudanar da aikin ƙasar yadda ya kamata.
Ya kuma ƙara tabbatar da cewar adadin yana da alaƙa don biyan buƙatun al’umma.